Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas

Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas

  • Bayyanar bidiyon sojoji suna raka yara zuwa makaranta a arewa maso gabas a Najeriya ya taba zukatan jama’a da dama
  • Yanzu ‘yan bindiga sun mayar da hankalinsu kacokan akan daliban makaranta don har yanzu akwai wasu a hannunsu
  • Sakamakon hakanne wasu jihohi suka umarci a rufe makarantun sakandare na wani lokaci kafin a samu zaman lafiya da tsaro

Arewacin Najeriya - Bidiyon sojoji suna raka wasu daliban makaranta zuwa makaranta a arewa maso gabas a Najeriya ya taba zukatan mutane da dama.

Yanzu ‘yan bindiga sun fi harin daliban makaranta don har yanzu akwai sauran dalibai a hannun masu garkuwa da mutane bayan sun sacesu daga makarantunsu.

KU KARANTA: Mai Shari'a Garba, babban alkalin FCT yayi murabus, ya bayyana dalili

Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas
Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sakamakon cigaba da satar dalibai, jihohi da dama suka rufe makarantun sakandare na wani lokaci, shafin Linda Ikeji ya ruwaito

Sojoji sun fara raka yara makaranta

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama

Don samar da kariya ga dalibai, sojojin Najeriya sunyi tsiri tsayawa kusa da makarantu amma duk da haka wasu makarantun babu tsaro.

A wani bidiyo wanda ya bayyana babu dadewa an ga yadda sojoji suke raka yara makaranta don tabbatar da isarsu lafiya.

KU KARANTA: Jiragen NAF sun ragargaji motocin yakin Boko Haram, sojin kasa sun sheke 'yan ta'adda

Abinda ya hana mu ceto daliban makarantar Tegina, Gwamnatin Neja

Gwamnatin jihar Neja ta bayar da dalilan da zasu iya janyo bacin lokaci wurin ceto yaran makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina.

Yayin da sakataren jihar, Ahmed Matane, yake tattaunawa da ThisDay a ranar Litinin, ya bayyana yadda iyayen yaran suka dakatar da amfani da sojoji wurin ceto yaran.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta so amfani da sojoji wurin shiga dajin su bude wuta su ceto yaran amma iyayen yaran sun dakatar dasu saboda gudun rasa rayukan yaran garin yin hakan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

A cewarsa:

Gwamnatin jihar ta so amfani da sojoji su tafi da makamai har cikin daji amma iyayen yaran sun roki gwamnati don kada su rasa yaransu garin karon batta.
Sun rokemu kuma sun bukaci a yi amfani da hanyar sasanci don ceto yaransu shiyasa muka dakata. Kun san irin wannan aikin zai iya janyo tashin hankali saboda kowa ya san ‘yan bindiga suna lura da yawonmu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel