Da Duminsa: Manyan Shugabannin PDP Na Kasa 7 Sun Yi Murabus
Rikicin da ke faruwa a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya dauki sabon salo a yayin da wasu shugabanni na kasa su bakwai su ka yi murabus, Daily Trust ta ruwaito.
Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar na kasa, Kwanel Austin Akobundu (mai murabus) ya tabbatar da murabus dinsu a ranar Talata amma bai bada cikakken bayani ba.
Wadanda suka yi murabus din sun hada da mataimakin sakataren watsa labarai na kasa, mataimakin mai bada shawara a bangaren shari'a, mataimakiyar shugaban mata, da wasu, inda suka ce 'rashin adalci' da shugaban jam'iyyar ya ke musu yasa suka fice, Vanguard ta ruwaito.
Uche Secondus, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, wanda wa'adinsa zai kare a karshen watan Disamba, yana fuskantar matsin lamba ya yi murabus.
Shugaban jam'iyyar na kasa ya samu sabani da na hannun damansa Nyesome Wike na jihar Rivers har ya soke shi a bainar jama'a.
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue shima ya yi kokarin sasanta mutanen biyu amma ba bu tabbas sun idan sun shirya.
Kafin rashin jituwansa da Wike, Kassim Afegbua, jigon jam'iyyar PDP a jihar Edo, ya yi kira ga Secondus ya yi murabus saboda yadda ya ke mulkar jam'iyyar.
Ya zarge shi da rashawa har ya yi kararsa a kotu.
Secondus ya kuma yi karar Afegbua a kotu kan bata masa suna.
Gwamna David Umahi (Ebonyi), Ben Ayade (Cross Rivers) da Bello Matawalle (Zamfara) sun bar PDP sun koma jam'iyyar APC.
Wannan ya sa wasu mambobin jam'iyyar da dama sun karayya da shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin Secondus.
A watan Yuli, dan majalisar wakilai na tarayya, Rimande Shawulu, ya bukaci Secondus ya yi murabus saboda gaza hana yan jam'iyyar ficewa.
Ba a samu ji ta bakin, Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun jam'iyyar ba a lokacin hada wannan rahoton.
Ku saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng