Manyan jami’an jam’iyyar PDP na kasa 7 sun yi murabus daga mukamansu

Manyan jami’an jam’iyyar PDP na kasa 7 sun yi murabus daga mukamansu

  • Rikicin shugabanci a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya kara yin muni a ranar Talata, 3 ga watan Agusta
  • Hakan ya kasance ne bayan jami'an jam'iyyar na kasa guda bakwai sun yi murabus daga mukamansu
  • Sun yi zargin cewa shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus yana masu rashin adalci

Abuja - Jami’an jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa su bakwai sun yi murabus daga mukamansu.

Manyan jiga-jigan jam'iyyar sun bayyana hakan ne a cikin wasiku daban-daban da suka aika wa sakataren jam'iyyar na kasa a ranar Talata, 3 ga watan Agusta.

Da dumi-dumi: Manyan jami’an jam’iyyar PDP na kasa 7 sun yi murabus daga mukamansu
Rikicin shugabanci na kara muni a PDP Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sun yi zargin cewa shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus ya yi masu rashin adalci, Channels Television ta ruwaito.

Sun yi alkawarin ci gaba da kasancewa masu biyayya ga PDP amma sun ce ba za su iya yin aiki tare da kwamitin aiki na jam’iyyar na kasa (NWC) ba, kamar yadda wata majiya ta cikin gida ta shaida wa TheCable.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Manyan Shugabannin PDP Na Kasa 7 Sun Yi Murabus

Daga cikin wadanda suka yi murabus akwai mataimakin sakataren kudi na jam’iyyar na kasa, mataimakin mai ba da shawara kan shari'a, mataimakin mai binciken kudi na kasa.

Sai kuma mataimakin sakataren yada labarai na kasa, mataimakiyar shugabar mata da mataimakin sakataren shirye-shirye.

Sun yi zargin cewa ba a bayyana lamuran da suka shafi kudi a jagorancin jam’iyyar.

Wani memba na NWC ya tabbatar wa jaridar TheCable batun murabus din amma ya ce za a fitar da sanarwa bayan wani taron gaggawa.

PDP ba sa'ar APC bace: PDP ta yi martani kan Jega bisa kwatanta ta da APC

A wani labarin kuma, Jam'iyyar PDP ta ce, ba daidai bane wani ya tsaya yana kwatanta nasarorinta da na jam'iyyar APC mai mulki a yanzu ba, jaridar Sun ta ruwaito.

Wannan na fito wa ne daga bakin kakakin ta na kasa, Kola Ologbondiyan a jiya Litinin 2 ga watan Agusta yayin da ya yake martani ga kalaman tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jiga-Jigan PDP Sun Shiga Taron Gaggawa Kan Wani Sabon Rikici da Ya Kunno

Legit.ng ta tattaro cewa Ologbondiyan ya ce yayin da PDP a cikin shekaru 16 na mulkinta ta biya bashin kasar tare da sake farfado da tattalin arziki gami da manyan ayyuka da aka samar ga 'yan kasa, APC ta lalata tattalin arzikin kasar ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel