Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan

Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan

  • Yayin da ake zargin jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu na jinya ne a birnin Landan
  • Wasu magoya bayansa sun bayyana hotunansa tare da gwamnan Lagos, Babajide Sanwo Olu
  • A halin yanzu, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana Landan domin duba lafiyarsa kamar yadda aka saba

London:- Jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu a Landan ranar Talata.

Tinubu ya jima baya ƙasar nan, inda ya tsallake muhimman ayyukan jam'iyyarsa ta APC, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A makonni biyu da suka gabata lokacin da aka gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar Lagos, Bola Tinubu bai samu halarta ba, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Rashin halarta jagoran siyasar a Najeriya kuma ɗan asalin jihar Lagos a wannan zaɓe ya jawo faruwar wasu abubuwa marasa daɗi.

Bola Tinubu da Gwamnan Lagos
Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hakanan kuma Tinubu bai dawo ba domin halartar tarukan jam'iyyar APC wanda aka gudanar a ƙarshen makon nan da ya gabata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fusatattun Daliban Wata Jami'an Sun Toshe Babbar Hanya Saboda Sheke Dan Uwansu

Yaushe Tinubu ya gana da gwamnan?

Sai dai a ranar Talata, wasu daga cikin masoyan Bola Tinubu sun buga hotunan jigon APC ɗin tare da gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu.

Magoya bayan Tinubu sun kara da cewa manyan masu faɗa aji na jihar Lagos ɗin sun gana ne ranar Talata a Landan.

Hakanan kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yanzu haka yana can birnin Landan ɗin domin duba lafiyarsa.

Hotunan Tinubu da gwamnan Lagos

Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Gwamnan Lagos
Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hotun Bola Tinubu da gwamnan Lagos
Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani labarin kuma Yan Fansho Sun Aike da Wata Muhimmiyar Wasika Ga Shugaba Buhari

Wasikar ya

n fanshon dai godiya ce da fatan alkairi biyo bayan biyansu wasu kuɗaɗe da suke bin gwamnatin tarayya bashi da shugaban yayi.

BBC Hausa ta ruwaito cewa takardar wasikar wacce take ɗauke da sanya hannun shugaban yan fansho na kasa, Elder Actor Zal, da kuma sakatarensa, sun jinjina wa shugaba Buhari bisa wanna namijin kokari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel