Babu Yaren da FG Take Fahimta Sosai Kamar Yajin Aiki, Kungiyar Likitoci Ta Yi Karin Haske
- Kungiyar likitoci NARD ta bayyana cewa babu wani abu da gwamnati ta yi tun bayan dakatar da yajin aikinsu
- Shugaban ƙungiyar, dakta Akanimo Ebong, shine ya faɗi haka ranar Litinin a Abuja
- Yace tun bayan 10 ga Afrilu ba su sake jin ɗuriyar gwamnati ba dangane da tattaunawa kan bukatunsu
FCT Abuja:- Shugaban ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NARD), Dakta Akanimo Ebong, yace FG bata nemansu a tattauna har sai sun tsunduma yajin aiki.
Shugaban yayi wannan jawabi ne yayin da yake zantawa da kafar watsa labarai ta Channels tv a shirinta na 'Sunrise Daily' ranar Litinin.
Ƙungiyar NARD ta sanar da fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 2 ga watan Agusta saboda gazawar gwamnati na biyansu albashi da kuma wasu alawus.
Me yajin aikin ka iya haifarwa?
A baya dai ƙungiyar ta gudanar da makamancin wannan yajin aikin a watan Afrilu, inda suka bar marasa lafiya ba tare da an duba su ba a asibitocin gwamnati dake faɗin ƙasar nan.
Sai dai an janye yajin aikin kwanaki 10 da fara shi bayan shugabannin ƙungiyar sun gana da wakilan gwamnati.
Wane cigaba aka samu tun bayan janye wancan yajin aikin?
Shugaban NARD, Dakta Ebong, ya bayyana cewa babu wani mataki na azo a gani da gwamnatin tarayya ta ɗauka tun bayan janye yajin aikinsu a baya.
Punch ta ruwaito likitan na cewa:
"Maganar gaskiya bamu jin duriyar gwamnati har dai idan mun tsunduma yajin aiki, saboda haka mun koma yajin aikin mu yau. Daman can ba janye wa mukai baki ɗaya ba, mun dakatar da shi ne domin tattaunawa."
"Tunda muka dakatar da yajin aiki a ranar 10 ga watan Afrilu, babu wani abu da gwamnati ta yi, to yanzun mun koma."
"Kun sani mun bada lokacin da ya kamata domin a tattauna a samu matsaya, kuma mun yi kokarin duk da yakamata amma dai sai da abun ya ci tura muka koma yajin aiki yanzun."
A wani labarin kuma Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari
Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ƙalubalanci tsohon gwamna Sule Lamido, ya fito ya bayyana yadda Saminu Turaki ya sallama masa tikitin takarar gwamna a 2007.
Lamido ya yi Allah wadai da karbar da Buhari yakewa gwamnoni da yan majalisu a fadar shugaban ƙasa idan suka sauya sheka zuwa APC.
Asali: Legit.ng