Muna Iya Kokarin Mu Duk da Yanayin da Ake Ciki, Gwamna Ya Koka da Karancin Kudin Shiga
- Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya ziyarci jihar Neja domin kaddamar da wata hanya da gwamnan jihar ya yi
- Gwamnan ya jinjina wa takwaransa na Neja, Abubakar Bello, bisa wannan namijin kokari
- Fayemi ya kara da cewa duk da ɗan karamin abinda suke samu a gwamnatance amma gwamnoni suna iyakar kokarinsu
Minna, Niger:- Shugaban kungiyar gwamnonin ƙasar nan kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yace gwamnoni suna iyakar kokarin da zasu iya duk da karancin kuɗaɗen shiga.
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin jawabi a wurin kaddamar da hanya mai kilomita 4.3Km a Minna, babban birnin jihar Neja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Fayemi ya bayyana cewa takwaransa na jihar Neja ya na zuba wa mutanensa romon demokaradiyya.
Yace a matsayinsa na wanda ya yi shugabanci lokacin da mai ke da daraja da kuma yanzun da yayi mummunar faɗuwa ba abinda zai iya cewa sai jinjina ga gwamnoni da suke kokari duk da yanayin da ake ciki.
Fayemi ya yaba wa gwamnan Neja
Kayode Fayemi ya kara da cewa gwamna Abubakar Sani Bello, mutum ne kamar shugaba Buhari wanda idan suka tunkari abu sai sun kammala shi.
Wani sashin jawabinsa yace:
"Mun kawo wannan matsayin ne domin mu cika abinda muka faɗa, ƙasar mu na cikin wani yanayi amma duk da haka tsayayyun gwamnoni suna kokarin aiwatar da abinda mutanensu ke bukata."
"Kuma Gwamna Bello yana daga cikin waɗanda suka kware wajen tattali idan ana maganar yanayin rashin isassun kuɗin shiga."
"Wannan kaɗan ne daga cikin abinda muka koya daga jagoranmu, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, domin ya sadaukar da kansa wurin kawo cigaba kala daban-daban a kasar nan."
Gwamna Feyemi ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban gwamnonin kasar nan yasan duk abinda ke faruwa na samun kudaden shiga ga kowane gwamna.
Yace amma duk da haka gwamnan Neja na kokarin aiwatar da bukatun mutune sabida haka dole a jinjina masa.
A wani labarin kuma Ba Da Jimawa Lamarin Yan Gudun Hijira Zai Zama Tarihi a Jihar Borno, Gwamna Zulum
Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa ba da jimawa ba lamarin yan gudun hijira zai zama tarihi.
Zulum ya faɗi hakane yayin wata ziyara da yakai sansanin yan gudun hijira dake Marte ranar Lahadi, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng