Yan bindiga na zanga-zanga kan sauke Sarki a Zamfara – Sanata Dansadau

Yan bindiga na zanga-zanga kan sauke Sarki a Zamfara – Sanata Dansadau

  • Yan bindiga a Zamfara sun kai farmaki garin Dansadau don nuna fushinsu kan sauke sarkin garin, Alhaji Hussaini Umar, da gwamnatin Jihar ta yi
  • Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ne ya bayyana hakan a wata hira ta wayar tarho
  • Ya ce hakan na nuni ga cewa lallai gwamnan yana da hannu a tuhumar da ake masa na kasancewa da hannu a ayyukan ta'addanci

Wani tsohon sanatan Zamfara, Saidu Dansadau ya ce 'yan bindiga na kara kai hare -hare kan al'ummar Dansadau don nuna rashin amincewarsu da dakatar da Sarki Hussaini Umar, da ake zargi da hannu a ta’addanci.

Gwamnatin jihar ta dakatar da Umar ne a watan Yuni bisa zarginsa da hannu a ayyukan ta'addanci.

Yan bindiga na zanga-zanga kan sauke Sarki a Zamfara – Sanata Dansadau
Sanata Dansadau ya ce Yan bindiga na zanga-zanga kan sauke Sarki a Zamfara Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Dansadau, wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya daga 1999 zuwa 2007, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa karuwar hare-haren da ake kaiwa al’umma na nuna cewa sarkin da aka dakatar yana da hannu a hare-hare da satar shanu da ‘yan bindiga ke yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Ya ce:

“Yan bindigan suna gaya wa wadanda suka sace cewa garin Dansadau ba zai san zaman lafiya ba har sai an sake dawo da sarkin. Wannan a bayyane yake nuna cewa shawarar da hukumomi suka yanke na cire sarkin yayi daidai.

“Sarkin yana da hannu a cikin abin da ‘yan fashi da makami da barayin shanu ke yi, in ba haka ba me zai sa su yi zanga -zangar adawa da cire shi. Wannan yana tabbatar da cewa yana da alaƙa da su.

“Kwamitin da aka dora wa alhakin binciken sarkin ya kamata ya gaggauta daukar mataki sannan ya mika rahotonsa ga hukuma.

“Yanzu haka sarkin na tsare, wayoyinsa da kayan aikin ofisoshinsa duk gwamnati ta kwace. Bai kamata gwamnati ta biye wa wadannan miyagun mutane ba.”

A watan Yunin wannan shekarar ne Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da tumbuke sarkin bisa zargin alaka da ’yan bindiga, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode

Sannan gwamnan ya kafa kwamiti karkashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, DIG Ibrahim Mamman Tsafe, don gudanar da bincike kan sarkin.

'Yan bindiga sun kutsa asibiti a jihar Zamfara

A wani labarin, mun ji cewa wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.

Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel