Ba Da Jimawa Lamarin Yan Gudun Hijira Zai Zama Tarihi a Jihar Borno, Gwamna Zulum

Ba Da Jimawa Lamarin Yan Gudun Hijira Zai Zama Tarihi a Jihar Borno, Gwamna Zulum

  • Gwamna Zulum na jihar Borno ya sha Alwashin maida kowane ɗan gudun hijira gidansa
  • Gwamnan yace da sannu lamarin yan gudun hijira a jihar Borno zai zama tarihi idan Allah ya so
  • Farfesa Zulum ya faɗi haka ne yayin wata ziyara da ya kai sansanin yan gudun hijira dake Marte

Borno:- Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa ba da jimawa ba lamarin yan gudun hijira zai zama tarihi.

Zulum ya faɗi hakane yayin wata ziyara da yakai sansanin yan gudun hijira dake Marte ranar Lahadi, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

Wannan na cikin kokarin da gwamnatinsa ke yi na maida yan gudun hijira zuwa yankunan su musamman inda aka samu tsaro.

Zulum yace: "Da sannu zamu maida kowa gidansa. Nan gaba labarin yan gudun hijira zai zama tarihi idan Allah ya so."

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum
Ba Da Jimawa Lamarin Yan Gudun Hijira Zai Zama Tarihi a Jihar Borno, Gwamna Zulum Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kashin farko na mutanen dake zaune a sansanin Marte sun fara komawa gidajensu dake Dikwa, Monguno da Maiduguri tun 30 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari

Shin hakanan gwamnati ke maida su gida ba tare da tallafa musu ba?

A kashin farko na kimanin mutane 2,870 da suka koma an samar musu da gidaje 500 ƙarƙashin shirin ƙungiyar raya tafkin Chaɗi.

Bayan an basu gidajen zama, Gwamnati ta raba tallafin buhun shinkafa, buhun masara da jarkan mai ga kowane magidanci.

Da yawan mutanen da aka maida gida ba su da wata sana'a da ta wuce noma domin sai sun yi noma suke samun abincin da zasu ci.

Inane Marte?

Marte na ɗaya daga cikin garuruwan da yan ta'adda suka mamaye a baya, wanda hakan yasa mazauna garin suka tsere daga yankin.

Sai dai daga baya dakarin sojojin Najeriya tare da haɗin guiwar jami'an sa kai na yankin sun samu nasarar korar yan ta'addan.

Kotu ta sake ɗage karar hadiman Igboho

A wani labarin kuma Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

Babbar kotun tarayya Abuja ta ɗage sauraron karar hadiman Sunday Igboho har zuwa ranar Laraba 4 ga watan Agusta, 2021, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mai shari'a Egwuatu ya baiwa lauyan mutanen, Pelumi Olagbenjesi, damar wannan matakin domin ya gyara sunayen waɗanda yake karewa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel