Abdulrasheed Bawa: EFCC ta lissafa nasarorin sabon shugabanta bayan kwanaki 100 a ofis

Abdulrasheed Bawa: EFCC ta lissafa nasarorin sabon shugabanta bayan kwanaki 100 a ofis

  • Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya cika kwanaki 100 a kan kujerar shugabanci
  • Domin murnar hakan, hukumar ta EFCC ta jero tarin nasarorin da Bawa ya samu a cikin wadannan kwanaki
  • Shugaba Buhari ya nada Bawa a watan Fabrairu domin ya shugabanci hukumar bayan ficewar Ibrahim Magu

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta lissafa nasarorin da shugabanta, Abdulrasheed Bawa ya samu, domin murnar cikarsa kwanaki 100 a kan mulki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Bawa a watan Fabrairu domin ya shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa bayan ficewar Ibrahim Magu.

Abdulrasheed Bawa: EFCC ta lissafa nasarorin sabon shugabanta bayan kwanaki 100 a ofis
Abdulrasheed Bawa ya cika kwanaki 100 a ofis Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Ga jerin nasarorin da Bawa ya samu a cewar EFCC:

1. An kwato N6,142,645,673.38 (sama da Naira biliyan 6), $ 8,236,668.75, £ 13,408.00, da € 1,730.00, dalar Kanada 200, CFA374,000.00, ¥ 8,430.00 (Yen na kasar Japan)

Kara karanta wannan

MURIC ta yi martani ga CAN: 2023 ba lokacin Shugaban kasa Kirista bane

2. An kwato motoci 25, jirgin ruwa guda biyar, babura biyu, shago daya, filaye shida, kafet daya, kayan lantarki 13, kadarori 30, masana'anta daya, gidan mai guda daya.

3. An kwato manyan kayayyakin man fetur

4. An tabbatar da hukunci 185 daga kararraki 367 da aka shigar a fadin ofisoshin shiyya

Manyan ayyuka

1. Gyarawa da samar da kayan koyarwa na makarantar horarwa na hukumar, makarantar EFCC, Karu, Abuja.

2. Gyaran Ginin Hedikwatar Abuja, Benin, Gombe, Lagos, Fatakwal da Ofishin Shiyyar Uyo.

3. Gina Dakin Binciken na’ura na sabon sashin Leken Asiri da aka samar.

4. Gina karin ofisoshi a Benin, Enugu, Kaduna, Ibadan, Maiduguri, Sokoto da ofisoshin shiyyar Uyo.

5. Gina Cibiyar nazari na TOC a Ofishin Shiyyar Legas.

6. Raba motocin aiki da motocin daukar marasa lafiya da aka saya don inganta ayyukan hukumar, da sauran su.

EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Kara karanta wannan

Ayi hattara, sabon samufurin COVID-19 ya shiga Abuja, da wasu Jihohi 7 inji Gwamnatin Tarayya

A gefe guda, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta ƙaddamar da wata sabuwar manhaja da zata taimakawa yan Najeriya wajen tura rahoton aikata laifin cin hanci cikin sauƙi.

Shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa, wanda ya ƙaddamar da 'Manhajar Eagle Eye' a Abuja ranar Laraba, yace manhajar zata ba da damar ɗaukar hotuna da wuraren da ake zargin ana aikata laifuka, kamar yadda punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng