Yanzu: Rikici ya barke tsakanin dan Shi'a da mazauna a Kano, ya jawo kone-kone

Yanzu: Rikici ya barke tsakanin dan Shi'a da mazauna a Kano, ya jawo kone-kone

  • Wani rikici ya barke tsakanin mazauna a wani yankin jihar Kano saboda banbancin ra'ayin addini
  • Rahoton ya ce an kone motar wani dan shi'a da yaki sayar da filinsa ga al'ummar unguwa saboda wasu dalilai
  • A halin yanzu, rundunar 'yan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin, wanda ya jawo rikici cikin al'umma

Jihar Kano - Wani rikici da ya ɓarke a ƙwaryar birnin Kano ya haddasa ƙone-ƙone a yammacin ranar Litinin, BBC Hausa ta ruwaito.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani game da abin da ya haddasa rikicin da ya faru a unguwar Dorayi Babba.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda aka kona wata mota da kuma mutane sun yi carko-carko.

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke a jihar Kano, ya jawo kone-kone
Taswirar jihar Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mazauna unguwar sun shaida cewa rikicin ya samo asali ne tsakanin wani mutum mabiyin Shi'a da makotansa sakamakon fili da ya mallaka a unguwar.

A cewarsu, wasu mazauna unguwar ne ke adawa da taron da mabiya Shi'a ke gudanarwa a filin nasa kuma suka nemi a daina.

Kara karanta wannan

Da duminsa: IGP ya maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu

Rundunar 'yan sandan Kano ta ce sai nan gaba za ta bayar da bayanin abin da ya faru idan ta kammala bincike.

A cewar mazauna yankin:

"Bayan ya kin dainawa sai mutanen suka yi tayin sayen filin nasa kan miliyan 12 amma ya ce ba zai sayar ba, suka ce miliyan 15, nan ma ya ce a'a.
"Mutumin ya ce shi sai miliyan 50 zai sayar da filin. Daga baya ya sake tara mutane don ci gaba da taron Shi'a. Shi ne mutane suka fusata suka kona motarsa."

Jim kadan baya sake Zakzaky da matarsa, sun cilla wani boyayyen wuri a Abuja

Shugaban kungiyar Musulunci ta Islamic Movement in Nigeria (IMN) Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat, sun bar jihar Kaduna zuwa wani wurin da ba a bayyana ba a cikin babban birnin tarayya, Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan El-Zakzaky da matarsa Zeenat sun sake samun ‘yanci a ranar Laraba 28 ga watan Yuli daga Cibiyar Gyaran Hali da ke Kaduna biyo bayan sallamar da babbar kotun jihar Kaduna ta yi musu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari wani kauye, sun yiwa mai gari yankan rago

Lauyan su, Femi Falana (SAN), a ranar Laraba ya fadawa SaharaReporters cewa malamin da matarsa sun bar Kaduna zuwa wani wurin da ba a bayyana ba bayan sun kwashe shekaru biyar a tsare ba bisa ka'ida ba.

Cikakken Bayani: Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

A wani labarin, rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran 'yan jarida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.