Zamu Tona Asirin Yan Ta'addan Cikin Mu, Shugabannin Fulani Sun Yi Alakawari

Zamu Tona Asirin Yan Ta'addan Cikin Mu, Shugabannin Fulani Sun Yi Alakawari

  • Shugabannin fulani a jihar Taraba sun sha alwashin bankaɗo masu aikata laifuka daga cikin su
  • Fulanin sun ɗauki wannan alƙawarin ne yayin wani taro da suka halarta a fadar sarkin Muri
  • Shugaban Miyetti Allah reshen jihar yace fulani sun amince su tona asirin yan ta'adda ko da ƴaƴansu ne

Taraba:- Shugabannin Fulani makiyaya na jihar Taraba sun yi alƙawarin bankaɗo bara gurbin cikin su a cikin watanni biyar, kamar yadda dailytrust hausa ta ruwaito.

Fulanin sun ɗauki wannan alkawarin ne a wani jawabi da suka fitar bayan sun halarci wani taro a fadar mai martaba Sarkin Muri dake Jalingo, kamar yadda Pm News ta ruwaito.

Daga ɓangaren gwamnatin jihar, Taron ya samu halartar mai baiwa gwamna shawara kan tsaro, Darius Ishaku.

Fulani sun yi alakwarin tona asirin bara gurbin cikinsu
Zamu Tona Asirin Yan Ta'addan Cikin Mu, Shugabannin Fulani Sun Yi Alakawari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wane mataki fulanin zasu ɗauka?

A jawabin, shugaban ƙungiyar fulani miyetti Allah na reshen Taraba, Sahabi Tukur, yace makiyaya sun ɗauki alkawarin tona asirin yan ta'addan cikinsu ko da kuwa 'yayansu ne ko yan uwansu.

Kara karanta wannan

Babu Yaren da FG Take Fahimta Sosai Kamar Yajin Aiki, Kungiyar Likitoci Ta Yi Karin Haske

Wani sashin jawabin yace:

"Za'a tantance tare da gano waɗanda suke aikata laifin domin su tuba, waɗanda kuma suka yi taurin kai zamu mika su ga jami'an tsaro."
"Wannan aiki ne mai matukar wahala, amma kusan ya zama wajjibi a gare mu domin dawo da martabar fulani makiyaya wadda wasu bara gurbi suka bata mana."

Shugaban makiyayan ya kuma tabbatarwa sarkin Muri cewa fulani a shirye suke wajen taimakawa duk wani mataki da zai zakulo bara gurbin cikin su.

Ku fito da bara gurbin cikinku

Yayin wata ganawa da shugabannin Fulanin Taraba a makon da ya gabata, Sarkin Muri, ya umarce su da su fito da yan ta'addan cikinsu.

Sarkin yace ya zama wajibi ne ya ɗauki wannan matakin duba da yadda matsalar tsaro ke kara taɓarɓarewa a yankin da yake jagoranta.

Hakazalika, Sarkin ya koka kan yadda wasu bara gurbi daga cikin fulani suka zubar da kimarsu a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo Najeriya

A wani labarin kuma Babu Yaren da FG Take Fahimta Sosai Kamar Yajin Aiki, Kungiyar Likitoci Ta Yi Karin Haske

Shugaban ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NARD), Dakta Akanimo Ebong, yace FG bata nemansu a tattauna har sai sun tsunduma yajin aiki.

Ƙungiyar NARD ta sanar da fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 2 ga watan Agusta saboda gazawar gwamnati na biyansu albashi da kuma wasu alawus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262