Bayan dakatar da Abba Kyari, Singham ya yi zazzafan martani kan 'yan sanda
- Tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Wakili ya yi martani kan dakatar da Abba Kyari
- Ya jaddada cewa, abin da hukumar 'yan sanda ta yanke shi ne daidai kuma nan ne za a gano gaskiya
- Ya kuma bayyana cewa, watakila ma wani ne ke kokarin ganin bayan Abba Kyari saboda bai son aikinsa
Jihar Gombe - Tsohon Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano CP Muhammad Wakili (mai ritaya) ya ce dakatar da DCP Abba Kyari da kuma kaddamar da bincike kan zargin da ake yi masa da hukumar kula da aikin 'yan sanda ta yi shi ne matakin da ya fi dacewa a dauka don sanin gaskiyar lamarin.
A jiya ne dai Hukumar ta dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda sakamakon zargin hannu a wata damfara da Hukumar Binciken Manyan Laifukka ta Amurka (FBI) ke yi masa.
Hukumar kula da ayyukan 'yan sandan ta dauki matakin dakatar da mataimakin kwamishinan 'yan sandan ne, bayan shawarar da babban sufeto janar Usman Alkali Baba ya bayar.
BBC Hausa ta tambayi CP Muhammad Wakili, kwamishinan 'yan sanda mai ritaya a Najeriya, wanda aka sani da Singham ko mene ne mataki na gaba bayan dakatarwar?
CP Wakili ya amsa da cewa, ba za a iya cewa komai yanzu ba har sai bincike ya kammala, abin da ka iya biyo baya kuwa, a cewarsa ya danganta da abin da ya zo daga rahoton da masu bincike suka gabatar.
Hakazalika, da aka tambaye shi ko za a iya samun adalci cikin binciken, ya jaddada cewa, dole ma a yi adalci, saboda wannan lamari ne da al'umma ke son ganin yadda zai kasance.
Ya kuma kara da cewa, bincike ne kadai zai iya tabbatar da Abba Kyari ya aikata laifi ko kuma wani ne a gefe da bai son kyakkayawan aikin da yake yi yake son ba ta sunansa.
Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan
Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda (DCP), na iya bayyana a gaban kwamiti na musamman da ke binciken zarginsa da hannu a zambar intanet a wannan makon, jaridar Punch ta ruwaito.
Ku tuna cewa hukumar kula da ayyukan 'yan sanda (PSC) a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta, ta dakatar da Kyari daga aiki kamar yadda sufeto janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, ya shawarta a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli.
PSC ta bayyana cewa za a dakatar da Kyari har sai an kammala bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta yi, in ji jaridar The Nation.
Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya
A wani labarin, A yayin da aka dakatar da shugaban rundunar IRT, Abba Kyari, Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Alkali Baba Usman ya gargadi dukkan jami'an da kada su kuskura su zubar da mutuncinsu a idon jama'a.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Usman, ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da ayyukan miliyoyin nairori da Olusoji Akinbayo, kwamandan runduna ta “B”, Apapa ya yi.
Shugaban 'yan sandan wanda ya samu wakilcin Johnson Kokumo, Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda (AIG) a sashen runduna ta 2 da ke jihar Legas, ya bayyana hakan ne a karshen mako.
Ya ce da zarar jami'i ya rasa goyon bayan jama'a to bai da wani dalilin da zai sadaukar da mutuncin ofishin sa.
Asali: Legit.ng