Da duminsa: IG na yan sanda ya bada umurnin kaddamar da bincike kan zargin da ake yiwa Abba Kyari

Da duminsa: IG na yan sanda ya bada umurnin kaddamar da bincike kan zargin da ake yiwa Abba Kyari

Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bayyana umurnin gudanar da bincike kan zargin da aka yiwa jami'in sanda DCP Abba Kyari.

Wannan na kunshe cikin jawabin da kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya saki da yammacin Alhamis, 29 ga Yuli, 2021.

A cewar Mba, hukumar na jaddadawa yan Najeriya cewa za'a bi gaskiya da adalci kuma za ta karfafa alakarta da takwararta na Amurka, FBI.

Franks Mba yace:

"Sakamakon zargi da tuhumar da hukumar FBI ta yiwa daya daga cikin jami'an yan sandan Najeriya, DCP Abba Kyari, Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba psc (+), NPM, ya bada umurnin duba abun."
"Duk yadda ta kaya za'a sanar da jama'a."

Da duminsa: IG yan sanda ya bada umurnin kaddamar da bincike kan zargin da ake yiwa Abba Kyari
Da duminsa: IG yan sanda ya bada umurnin kaddamar da bincike kan zargin da ake yiwa Abba Kyari
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel