Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Caccaki Gwamatin El-Rufa'i, Sun Fadi Makudan Kudin da Suka Biya

Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Caccaki Gwamatin El-Rufa'i, Sun Fadi Makudan Kudin da Suka Biya

  • Iyayen ɗaliban Bethel Baptist Kaduna da aka sace sun koka da halin ko in kula na gwamnatin Kaduna
  • Ɗaya daga cikin iyayen, Marcus Angwa, yace yanzun ba su da wata mafita illa komawa ga Allah
  • Wata mahaifiya daga cikin iyayen ta bayyana cewa sai da ta biya dubu N500,000 kafin a sako 'yarta

Kaduna:- Marcus Angwa, ɗaya daga cikin iyayen da aka sace yayansu a makarantar Bethel Baptist Kaduna, yace shi da yan uwansa sun koma ga Allah domin ya kuɓutar musu da yayansu.

The Cable ta ruwaito cewa yan bindigan sun sace ɗalibai 121 daga gidan kwanansu a a makarantar Bethel Baptis ranar 5 ga watan Yuli.

Sai dai a kwanakin nan ɓarayin sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suka sace tare da alƙawarin sako sauran kashi-kashi.

Iyayen ɗaliban Bethel Baptist sun koka
Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Caccaki Gwamatin El-Rufa'i, Sun Fadi Makudan Kudin da Duka Biya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake tattaunawa da Punch, Angwa yace iyayen sun gaji da halin ko in kula da gwamnatin Kaduna ta nuna wajen kubutar da ragowar ɗaliban.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Karin Daliban FGC Yauri da Aka Sace

Angwa yace:

"Mun gaji da maganar gwamnati, iyaye na kokarin su sannan zamu bar sauran ga Allah. Wannan yanayin abun damuwa ne kuma bamu taɓa ganin irin wanna ƙasar ba inda mutanen cikinta ba su da ikon yawo cikin kwanciyar hankali."
"Yayanmu sun bar gida domin neman ilimi, amma daga baya masu garkuwa sun sace su zuwa cikin daji, kuma gwamnati ta kasa yin komai. Gwamnati ta faɗa mana kada mu biya kuɗi amma babu wani mataki da ta ɗauka na dawo mana da yayanmu."
"Babu abinda ya ragewa iyaye illa su koma ga Allah domin shi kaɗai ne zai iya magance musu wannan matsalar. A halin yanzun babu wanda muka yi imani da shi sai Allah."

Har nawa iyayen suka biya kuɗin fansa?

Ɗaya daga cikin iyayen da ƴaƴansu suka kubuta, Esther Joseph, tace domin kuɓutar da ɗiyarsa sai da ta biya dubu N500,000.

Mahaifiyar tace har yanzun ɗiyarta na cikin tsoro, kuma bata iya bacci, Esther tace:

Kara karanta wannan

Yan Bindigan da Suka Sace Daliban Bethel Baptist Kaduna Sun Karya Alkawari, Sun Turo Sabon Sako

"Bata iya magana sosai, kuma saida na biya dubu N500,000 kuɗin fansa, ni bazawara ce ita kaɗai ce yarinyar da nake da ita."
"Bata iya cin abinci yadda ya kamata, kuma har yanzun tana cikin tsoro domin sai ta tashi da daddare ta ƙankame ni."
"Ta faɗa mun irin wahalar da suka sha a hannun ɓarayin, tace yan bindigan na sanya su ruwan sama ya buge su sannan kuma ku kwanta a taɓo."

A wani labarin kuma Wasu Dalibai Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Kebbi Sun Gudo Daga Sansanin Yan Bindiga

Ɗaliban biyu, mace da namiji, suna daga cikin gomman da yan bindiga suka sace a sakandiren gwamnatin tarayya (FGC) Yauri, jihar Kebbi.

Kakakin hukumar yan sanda ta jihar Zamfara, SP Muhammed Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Gusau ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel