Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Karin Daliban FGC Yauri da Aka Sace

Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Karin Daliban FGC Yauri da Aka Sace

  • Wasu ɗalibai guda biyu daga cikin waɗanda aka sace a FGC Yauri, jihar Kebbi sun kubuta daga hannun yan bindiga
  • Rahotanni sun bayyana cewa an gano ɗaliban ne a dajin Ɗansadau dake jihar Zamfara
  • Tun mako shida da suka gabata, wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗalibai da dama a FGC Birnin Yauri

Yauri, Kebbi:- Wasu ɗalibai biyu daga cikin waɗanda aka sace a makarantar sakandire a jihar Kebbi sun tsero daga sansanin yan bindiga, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Ɗaliban biyu, mace da namiji, suna daga cikin gomman da yan bindiga suka sace a sakandiren gwamnatin tarayya (FGC) Yauri, jihar Kebbi.

Rahoton channels tv ya nuna cewa jami'an yan sanda ne suka ceto ɗaliban a dajin Dansadau, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara.

Dalibai biyu daga cikin waɗanda aka sace a FGC Birnin Yawuri sun tsero daga hannun yan bindiga
Da Dumi-Duminsa: Wasu Dalibai Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Kebbi Sun Gudo Daga Sansanin Yan Bindiga Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar yan sanda ta jihar Zamfara, SP Muhammed Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Gusau ranar Lahadi.

Yace: "An ceto ɗaliban su biyu suna yawo a dajin yankin Ɗansadau, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara."

Shin an biya kuɗin fansa?

Babu wani cikakken bayani ko an biya kuɗin fansa domin kubutar da ɗaliban yayin da ake tantama kan ragowar mutum nawa ne a hannun ɓarayin.

Mako shida da ya gabata ne wasu yan bindiga suka mamaye makarantar FGC Yawuri, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da dama tare da malamai huɗu.

A lokacin harin, yan bindigan sun kashe wani jami'an hukumar yan sanda guda ɗaya.

Sace mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare a jihohin Zamfara, Kebbi da sauran jihohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

A wani labarin kuma Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Sake Kafa Dokar Kulle Saboda Sabuwar COVID19

Gwamnatin tarayya ta yi gargaɗin cewa Najeriya na gaf da faɗawa matsalar sake ɓarkewar annobar COVID19 a karo na uku a kwanakin nan.

Duk da an cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar amma an sami mutum 10 da suka harbu da sabon nau'in cutar da ake kira Delta COVID19.

Asali: Legit.ng

Online view pixel