Yadda Abba Kyari ya turawa Hushpuppi asusun bankin wani don tura masa kudi

Yadda Abba Kyari ya turawa Hushpuppi asusun bankin wani don tura masa kudi

  • Wasu sabbin takardu sun nuna yadda Abba Kyari ya turawa Hushpuppi Akawunt Lamba
  • Abba Kyari ya ce dai shi bai karbi kudi hannun Hushpuppi ba
  • Hukumar FBI a Amurka ta alanta neman Abba Kyari ruwa a jallo

Sabbin bayanai sun bayyana kan zargin da aka yiwa hazikin jami'un dan sanda, DCP Abba Kyari, a gaban kotun kasar Amurka.

Legit ta ruwaito muku cewa kotun Amurka ta ce shahrarren dan damfara, Abbas Ramoni, wanda akafi sani da Hushpuppi ya ambaci Abba Kyari cikin wadanda suka sha romon kudin damfarar $1.1m.

Kyari kuwa a martaninsa, ya karyata wannan zargi inda yace ko kadan bai bukaci kudi hannun Hushpuuppi ba kuma bai amsa kudi hannunsa ba.

Amma wani takardan kotun Amurka da Vanguard ta gani, ya bayyana yadda ake zargin Abba Kyari da tura akawunt lamba wani daban ga Hushpuppi don ya tura masa kudi.

Wani sashen jawabin takardan yace:

Kara karanta wannan

Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode

"A ranar 20 ga Junairu, 2020, abin zargi Kyari ya tura sakon waya ga UICC Abbas dauke da akawunt lamban mai sunan bankin Najeriya da sunan wani daban ba nasa ba, inda UICC Abbas zai tura kudin aikin daure wani VINCENT."

Yadda Abba Kyari ya yi turawa Hushpuppi asusun bankin wani don tura masa kudi
Yadda Abba Kyari ya yi turawa Hushpuppi asusun bankin wani don tura masa kudi
Asali: Facebook

Ya kamata Abba Kyari ya je Amurka, ya wanke kan shi kafin a damke shi inji HURIWA

Kungiyar Human Rights Writers Association of Nigeria wanda aka fi sani HURIWA ta yi magana game da zargin Abba Kyari.

Kungiyar HURIWA ta ba shahararren ‘dan sanda, Abba Kyari shawarar ya tafi kasar Amurka ya wanke kan shi a gaban kotu daga zargin da ake yi masa.

Jaridar The Nation ta rahoto HURIWA ta na wannan jawabi a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, 2021.

Jawabin kungiyar HURIWA:

“Amurka kasa ce da ta ke da damukaradiyya mai tsari, inda doka ta ke aiki. Saboda haka idan ana zargin ka da laifi, babu bukatar a wanke ka a gidan jaridu.”

Kara karanta wannan

DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai

“Abin da ya fi dace wa shi ne, kafin FBI ta yi amfani da jami’an Interpol su yi ram da kai, a matsayinka na mai cewa ka na da gaskiya, sai ka nemi jirgin da zai je Washington ko New York, ka tafi kotu, ka nemi lauyoyi su kare ka a gaban Alkali.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel