Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023

Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023

  • Kakakin kungiyar dattawan Arewa ya caccaki jam'iyyar APC kan yunkurin lalata Najeriya
  • Hakeem Abba Ahmad ya bayyana cewa, Najeriya za ta ruguje a hannun APC kafin 2023
  • Ya kuma ce, matsalolin Najeriya ba kawai 'yan bindiga da satar mutane bane, har ma shugabanni

Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya caccaki jam’iyyar APC, kan yadda take tafiyar da Najeriya, yana mai cewa nan da shekarar 2023, jam’iyyar da ke mulki za ta ruguza al’ummar da ta fi yawan jama’a a Afirka.

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels na Politics Today a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli.

A cewarsa, jam'iyyar siyasa ta gaba da za ta karbi ragamar shugabanci a 2023 za ta gamu da aiki na gyara kasar.

Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023
Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Baba-Ahmed ya ce kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu ba wai kawai sakamakon ayyukan 'yan bindiga da satar mutane ba ne, gazawar shugabanci ne matsalar.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

A kalamansa:

“Me zaku yi da 2023 saboda daga yanzu zuwa 2023, APC za ta ruguza kasar nan gaba daya.
“Za ku karbi kasar da ta ruguje gaba daya daga wata jam’iyya wacce ta samar da ita ta PDP kuma ta yaya za ku gyara kasar nan? Menene tsarinku game da abin da zai faru da Najeriya a 2023?"

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce wasu mutane a Najeriya na kokarin wargaza kasar saboda dalilai na son kai.

Premium Times ta ruwaito cewa Mohammed yayi wannan bayani ne a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli, a Abuja a taron gabatar da wani littafi.

Ya yi zargin cewa wasu abubuwa na kokarin kara tabarbarewar rikicin kabilanci da bambancin addini a Najeriya.

Jan Aiki: Shugaba Buhari zai gina manyan gidajen yari guda 3 a Kano da wasu jihohi

Kara karanta wannan

Talakawa na son Buhari: Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta cire rai a zaben 2023

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya za ta gina sabbin cibiyoyi guda uku wadanda za su iya rage cunkoso na gidajen gyaran hali a kasar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 23 ga watan Yulin 2021 a wajen bikin kaddamar da Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya, da ke Hedikwatar rundunar ta Jihar Osun, a Osogbo.

Mista Aregbesola ya ce za a gina sabbin wuraren ne a Karchi ta Abuja, Kano, da Bori a jihar Ribas.

A cewar Ministan, kowanne daga cikin cibiyoyin zai kasance yana da kotuna don shari’ar fursunoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel