Gara in dinga samun N5 a Najeriya a kan in fita kasar waje: Budurwa ta bada labarin wahalarta a kasar waje

Gara in dinga samun N5 a Najeriya a kan in fita kasar waje: Budurwa ta bada labarin wahalarta a kasar waje

  • Wata budurwa Aisha Ganiyu, mai shekaru 25 ta bayyana yadda ta kusa shiga harkar karuwanci a kasar Mali
  • An shawarceta da ta zagaya ta ratsa kasashe don neman aikin da yafi wanda take yi a Legas samu
  • A cewar Aisha, bayan abinda ta fuskanta a Mali bata tunanin zata kara zuwa kasar waje har abada

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Aisha Ganiyu ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a kasar Mali. A wani bidiyo na tattaunawa da aka yi da ita wanda LegitTV ta dauka, ta bayyana irin wahalhalun da ta fuskanta bayan tayi tafiya zuwa Mali.

Aisha ta bayyana yadda mutanen da suka yi mata sanadin zuwa Mali suka matsa mata lamba a kan sai ta fara karuwanci.

KU KARANTA: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223

Gara in dinga samun N5 a Najeriya a kan in fita kasar waje: Budurwa ta bada labarin wahalarta a kasar waje
Gara in dinga samun N5 a Najeriya a kan in fita kasar waje: Budurwa ta bada labarin wahalarta a kasar waje
Asali: Original

Basu so in dawo ba

A cewarta, basuso tafiyar ta ba bayan ta farga cewa aikinta na Legas yafi wanda ta samu a Mali. Ta ce bata marmarin komawa kasar waje har abada koda kuwa ta samu damar da tafi haka.

Kara karanta wannan

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullun

Budurwar ta kara da tabbatar wa da jama’a cewa gara ta bude shago ta dinga samun N5 a cikin kasarta akan ta tafi wani wurin.

Ya aka yi Aisha ta tsero zuwa kasarta ta gado?

Ta bayyana yadda aka yi ta gudo inda tace ta hadu da sauran mata wadanda suke cikin harkar karuwanci. Ta bazama tana rokon mutane har ta samu wadanda suka taimaka mata har ta koma Najeriya.

Matar ta bayyana yadda mahaifinta ya bata wuri don ta bude shago ta fara sabuwar rayuwa, yanzu haka tana bukatar kudade ne don ta siya abubuwa ta cika shagon dasu.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Shin da gaske 'yan Boko Haram na shigo da motocin yaki ta iyakokin Najeriya?

Marwa yayi jawabi ga jami'an NDLEA da aka karawa girma

Buba Marwa, shugaban NDLEA ya umarci jami’an tsaro da su ragargaji masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Marwa ya yi wannan maganar a ranar Laraba yayin wani taro na kara wa manyan jami'an NDLEA girma a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Amina ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari a dakinta, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure

A cewarsa wannan salo ne na musamman na yaki da harkar miyagun kwayoyi a kasar nan kuma hakan da alamu zai cimma nasara, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel