Rikicin jam'iyyar APC: Gwamna Matawalle ya ziyarci Marafa domin a yi sulhu

Rikicin jam'iyyar APC: Gwamna Matawalle ya ziyarci Marafa domin a yi sulhu

  • Gwamnan jihar Zamfara ya gana da Marafa domin dinke barakar dake tsakaninsu na siyasa
  • A baya an samu rikici a jam'iyyar APC ta jihar Zamfara bayan da Matawalle ya sauya sheka zuwa APC daga PDP
  • Wasu daga cikin jiga-jigan APC na jihar Zamfara sun yi watsi da jagorancin gwamna Matawalle da gwamna Buni ya sanar

Kaduna - Gwamnan jihar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle ya ziyarci tsohon dan majalisar dattawa Sanata Kabiru Marafa domin sulhu kan rikicin da ya barke a jam'iyyar APC tun bayan da gwamnan ya shiga cikinta a watan Yuni.

Gwamnan ya ziyarci Sanata Mafara ne a gidansa da ke Kaduna ranar Asabar.

A wata gajeriyar tattaunawa da BBC Hausa, Sanata Marafa ya ce gwamnan ya ziyarce shi ne domin warware rikicin da ya cakude tun bayan sauya shekarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Rikicin jam'iyyar APC: Gwamna Matawalle ya ziyarci Marafa don sulhu
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta yaya rikici ya kunno kai tsakanin Marafa da Matawalle?

Kara karanta wannan

Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari

Rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu ne bayan da Sanata Marafa da tsohon gwamnan Zamfara Abdul Aziz Yari suka yi fatali da kalaman shugaban riko na jam'iyyar ta APC, Maimala Buni, cewa Gwamna Matawalle shi ne jagoran APC a Zamfara.

Sai dai Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa - wadanda gwamnan ya tarar a cikin jam'iyyar ta APC - sun ce ba za su yarda a yi musu hawan kawara ba haka kawai ba.

Abdulaziz Yari ya ce:

"Abu guda ne ba mu yarda da shi ba, inda shi Gwamna Maimala ya ce [Matawalle ne jagoran APC] domin babu shi a cikin tattaunawarmu wadda muka yi da gwamnoni guda shida.

Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin wannan mataki na ziyartar Sanata Marafa da Gwamna Matawalle ya yi zai zama sanadin dinke barakar da ke tsakaninsu.

Rikici: Mataimakin gwamna na kokarin karbe kujerar Matawalle, PDP ta yi martani

An rahoto cewa Mahdi Aliyu Gusau, mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya samu goyon bayan jam’iyyar PDP don karbar kujerar Bello Matawalle a matsayin gwamnan jihar dake a arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Fani Kayode, Shehu Sani sun ziyarci gwamnan da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ana rade-radin za su bi sahu

Wannan ya biyo bayan sauya shekar da Gwamna Matawalle ya yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki tare da sauran zababbun masu rike da mukaman siyasa a jihar.

Sai dai, Gusau ya tsaya, yana mai cewa ba a zabe shi don ya fice daga PDP zuwa wata jam'iyyar ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya koka kan barazanar majalisa na tsige shi

A wani labarin, Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, ya ce majalisar dokokin jihar na ci gaba da shirin tsige shi a ranar Alhamis duk da cewa hakan ya saba wa doka da umarnin kotu, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai bayani a ofishinsa a ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, mataimakin gwamnan ya ce matakin da Majalisar Dokokin jihar ta dauka ya nuna rashin biyayya ga umarnin kotu kuma zai zama daidai da nuna rashin bin doka.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Zamfara ya sa kafar wando daya da ‘yan majalisa, ya ce ba zai gurfana a gabansu ba

A cewarsa:

“Kamar yadda kuka sani, jam’iyyata ta PDP, ta gabatar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tana kalubalantar dambarwar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara kamar yadda aka tsara a yanzu don fara batun tsigeni ko kuma duk wani batu da ake a kaina a matsayin wanda aka zaba a karkashin jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel