Arewacin Najeriya na daya daga cikin wuraren da za'a shiga halin yunwa a duniya - Rahoto

Arewacin Najeriya na daya daga cikin wuraren da za'a shiga halin yunwa a duniya - Rahoto

Kungiyar abincin duniya WFP da kungiyar aikin noma ta duniya FAO sun lissafa Arewacin Najeriya daga cikin sabbin wuraren da za'a fi fama da yunwa a fadin duniya.

Kungiyoyin sun ce nan da watanni hudu, rikice-rikice, cutar COVID-19 da sauyin yanayi ka iya kara tsananin yunwa a Najeriya da wasu kasashen duniya 22.

Ms Eri Kaneko, mai magana da yawun Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ta bayyana hakan yayin hira da manema labarai a hedkwatar majalisar UN dake New York, ranar Juma'a kan rahoton.

Kaneko tace kasar Habasha da Madagascar ne kasashe biyu da ake tsoron yunwa zai fi shafa, a cewar rahoton.

Arewacin Najeriya na daya daga cikin wuraren da za'a shiga halin yunwa a duniya - Rahoto
Arewacin Najeriya na daya daga cikin wuraren da za'a shiga halin yunwa a duniya - Rahoto
Asali: Depositphotos

Tace:

"Kasashen da ka iya fuskantar wannan abu shine Sudan ta Kudu, Yemen, da Arewacin Najeriya. A wasu sassan kasashen nan, mutane da yawa na iya halaka sakamakon fari."
"Wasu kasashen da rahoton ya ambata zasu iyashiga halin yunwa sune Afghanistan, Burkina Faso,Central African Republic, Colombia, DR Congo, Haiti, Honduras, Sudan, da Syria,.’

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

A cewarta, WFP da FAO sun ce akwai bukatar kungiyoyin tallafi su kawo daukin gaggawa domin ceton rayukan mutane daga yunwa da fari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng