Bayani dalla-dalla: Yadda daina sayarwa yan kasuwan canji Dala zai shafi darajar Naira
- Babbar bankin Najeriya CBN ya haramta sayar da Dalar Amurka ga yan kasuwan canji (BDC).
- Yan Najeriya sun bukaci sanin shin me hakan ke nufi
Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya yiwa manema labarai bayan zaman kwamitin kudi MPC na bankin ranar Talata.
Ya ce N5. 7 billion da ake baiwa yan kasuwar canji ba zai yiwu a iya cigaba ba saboda kimanin yan kasuwan canji 5500 ake baiwa $110million kowani mako.
Tun lokacin, farashin Naira ya sauka 523/$ a kasuwar bayan fagge ranar Laraba, karo na biyu bayan saukar da yayi ranar Talatar.
A rahoton da aka gani a shafin naijabdcs.com, shafin yan kasuwar Canji, an sayi Dalar Amurka a farashin N515 kuma an sayar a N523 ranar Laraba.
Me hakan ke nufi?
Wakilin Legit Hausa ya zanta da wani masanin tattalin arziki na kamfanin One17 Capital Limited Mr Isma'il Rufai, wanda ya yi bayani dalla-dalla da fashin baki kan wannan mataki da CBN ya dauka.
Isma'il Rufa'i ya ce abinda wannan mataki ne CBN ke nufi shine gwamnati ta cire tallafin da take baiwa yan kasuwan canji na Dala a saukake, ba wai an hana yan kasuwan canji (BDC) aiki bane.
Ya kara da cewa daga yanzu duk wanda ke bukatar Dalar Amurka don amfani zai iya zuwa banki a sayar masa.
Yace:
"Abinda hakan ke nufi shine mutane masu bukatar Forex (Dala) shine zasu rika zuwa banki kai tsaye. Ba wai CBN na kokarin hana yan BDC (kasuwar canji) cin abinci bane, kawai dai CBN baza ta cigaba da basu Dala bane kamar yadda ta saba basu kowani mako."
"Abinda yasa haka shine CBN ta gano yan kasuwar canji na kasuwancin miliyoyin daloli kuma hakan ya wuce iyakar da aka saka musu."
"Daga yanzu yan kasuwan canji zasu iya sayan Dala amma CBN ba zata basu ba. Amma zasu iya samu daga wasu daidaikun mutane masu Dala a hannu suna bukatan canji, ko kamfanoni masu bukatar canji."
Wani tasiri hakan zai yi?
Isma'il yace manufar haka shine samar da farashin canjin dala zuwa Naira guda, sabanin yadda yake a baya inda na banki ya banbanta da kasuwar bayan fagge.
"Yanzu CBN zai rika la'akari da farashin canji guda ta yarda duk mai bukatar Dala don kasuwanci irinsu shigo da kayayyaki daga waje kuma yana da sahihan takardun tabbatar da hakan, zai iya samun Dala a saukake a farashi na misalin N410 sabanin kasuwan canji da zai saya sama da N500."
"Dama duk wani mataki da aka dauka zai fuskanci wasu kalubale, kalubalen farko na yanzu shine abinda ake fuskanta yanzu na tashin kudin."
"Hakazalika, daya daga cikin dalilan CBN na daukan wannan mataki shine zuba ido kan yadda abubuwa ke gudana a bankuna sabanin yadda yan kasuwar canji ke kara farashin suna samun makudan kudi dare guda kuma ba'a iya bibiya."
Asali: Legit.ng
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng