Waiwaye: Tarihin can da, zamanin da 'yan Najeriya suka fara sanya kaya 'Gwanjo'

Waiwaye: Tarihin can da, zamanin da 'yan Najeriya suka fara sanya kaya 'Gwanjo'

Ga wadanda basu da isassun kudade wajen sayen sabbin kayan sakawa kal, tsoffin kaya da aka yi amfani dasu, wadanda aka fi sani da 'Gwanjo' ko 'Okrika' a wasu sassan Najeriya; su ne zabi kan gaba wajen cin ado da fantamawa a gari.

Gwanjo ya rufa ma jama'a da dama asiri a Najeriya, musamman gayu mutanen Allah da suka kware wajen sanya kayan kasashen Turai. Saboda haka, lokaci ya yi da ya kamata mu kawo muku tarihin yadda aka fara amfani da Gwanjo a Najeriya.

Gwanjo kaya ne da suka shahara a Najeriya, kuma akan shigo da tulinsu ne daga kasashen waje, kamarsu Amurka da Burtaniya.

Kamar yadda @edquest_ng ya wallafa a shafin Instagram, sunan Okrika, wanda shine aka fara kiran Gwanjo dashi ya samo asali ne daga wani gari mai tashar jiragen ruwa da ake kira Okrika a jihar Ribas inda ake tunanin kasuwancin Gwanjo a nan ya samo asali.

Kara karanta wannan

Dabbobi Sun Fi Su Gata, Baƙar Wuya Suke Sha a Hannun DSS: Lauya Ya Faɗa Halin Da Muƙarraban Igboho Ke Ciki

Waiwaye: Tarihin da, lokacin 'yan Najeriya suka fara sanya kaya 'Gwanjo'
Yadda ake kasuwar gwanjo | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

An ce an fara kasuwancin Gwanjo a shekarun 1950 a yankin Okrika, wanda shi ne tashar jiragen ruwa tilo da ke iya shigo da kayan da aka yi amfani da su daga Turai.

Saboda tsadar sabbin kaya, Gwanjo ya kasance abin da ake tsananin bukata a shekarun 1950 saboda mutane da yawa ba za su iya sayen sabo ba.

Yadda Gwanjo ya karbu a wajen jama'a da dama a Najeriya

Akwai mutanen da suka fi son Gwanjo fiye da sabbin kaya saboda sun yi imani cewa kaya Gwanjo ya fi sabo inganci da kargo.

A yau, zaku sami Gwanjo a sassa daban-daban na kasar nan. Galibi akan ga kayayyakin zube a kasa a wasu sassan Najeriya. Mutane kan sunkuya su zabi wanda ya yi musu, sannan su kwada kafin su biya kudi su yi tafiyarsu.

Kamar dai yadda ya gabata, ana shigo da Gwanjo daga kasashen duniya daban-daban, musamman daga Burtaniya da Amurka.

Kara karanta wannan

Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji wani Gwamna

Kasar Larabawa ta kirkiri manhajar soyayya don hada aure daidai da tsarin Muslunci

A wani labarin na daban, Mahukunta a kasar Iran sun kaddamar da wata manhaja ta soyayya wadda suka ce nufinta shi ne ta saukake neman aure bisa tsarin addinin Musulunci, BBC Hausa ta ruwaito.

Hukumar yada manufofin addinin Musulunci ta kasar ce ta kirkiro manhajar mai suna Hamdam wadda ke nufin aboki ko abokiyar zama, AlJazeera ta ruwaito makamancin haka.

Manhajar tana amfani da basirar komfuta wajen hada wadanda suke son su yi aure, kodayake mata daya kacal aka amince wa namiji ya aura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel