Dabbobi Sun Fi Su Gata, Baƙar Wuya Suke Sha a Hannun DSS: Lauya Ya Faɗa Halin Da Muƙarraban Igboho Ke Ciki

Dabbobi Sun Fi Su Gata, Baƙar Wuya Suke Sha a Hannun DSS: Lauya Ya Faɗa Halin Da Muƙarraban Igboho Ke Ciki

  • Pelumi Olajengbesi, lauyan da ke kara mukarraban Sunday Igbobo su 12 da ke tsare hannun DSS ya koka kan halin da suke ciki
  • Olajengbesi ya ce dukkan wadanda ake tsare da su suna gudawa saboda wata mugunyar miya mai suna 'injin oyel' da ake basu suna cin tuwo da ita
  • Lauyan ya kuma kara da cewa a kasa suke kwana, sannan ga duka da azabtarwa duk da cewa mafi yawancinsu na da hawan jini

FCT, Abuja - Pelumi Olajengbesi, lauyan da ke kare mukarraban dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo aka Sunday Igboho su 12 ya yi ikirarin cewa ana ciyar da su wata mugunyar miya da ake kira 'injin oyel' a hannun DSS, The Punch ta ruwaito.

A cewar lauyan da ya ce ya tafi hedkwatar DSS da ke Abuja a ranar Juma'a, mutanen da ake tsare da su duk suna gudawa bayan cin miyan da tuwo ko eba. Ya kuma yi ikirarin ya shafe sati hudu kafin ya samu ganinsu.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: An tsare daliban Tegina da aka sace a sansanoni 25

Dabbobi Sun Fi Su Gata, Baƙar Wuya Suke Sha a Hannun DSS: Lauyan Ya Faɗa Halin Da Muƙarraban Igboho Ke Ciki
Mukarraban Sunday Igboho. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

An yi kokarin ji ta bakin kakakin DSS, Peter Afunanya, a kan ikirarin lauyan amma hakan bai yiwu ba domin bai amsa wayarsa ba da sakon kar ta kwana na sms da wakilin The Punch ya tura masa har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.

Wane hali mukarraban Igboho ke ciki? Lauyansu ya yi bayani

A wani karin bayanin da ya yi a ranar Juma'a, Olajengbesi ya ce shi da wasu lauyoyin biyu sun gana da mutum hudu cikin wadanda ake tsare dasu su 12 a yau.

Ya ce:

"Yana da muhimmanci na bayyana cewa halin da suke ciki keta hakkin bil-adama ne. Suna cikin lafiya da yanayi mara kyau.
"Ana barinsu suna kwana a kasa sannan akan yi musu mugun duka kafin daga bisani a basu magunguna don boye raunin da aka musu yayin azabtar da su.
"Musamman Lady K, da alama ta karye a kafarta na hagu kuma tana cikin tsananin ciwo. Bata canja kayanta ba kuma hakan nan ta ke nade kanta ta kwana a inda aka rufe ta.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno

"Mafi yawancinsu suna da ciwon hawan jini kamar yadda asibitin SSS ta tabbatar. Ana ciyar da su wani miya da ake kira 'injin oyel' tare da abincinsu. Abin da suke yi kawai shine su ci abinci su koma bayi suna gudawa.
"An bar su cikin mummunan hali, dabbobi ma sun fi su gata, muna iya kokarin mu ga mun kwantar musu da hankali kafin mu rabu da su."

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

A wani labarin daban, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel