Hoton Matar Ɗan Bindigan Katsina Da Aka Kama Da Tsabar Kuɗi N2.4m, Mijin Ya Tsere

Hoton Matar Ɗan Bindigan Katsina Da Aka Kama Da Tsabar Kuɗi N2.4m, Mijin Ya Tsere

  • Jami'an yan sandan Katsina sun kama wata matar dan bindiga dauke da tsabar kudi Naira miliyan 2.4
  • Matar mai suna Aisha Nura ta amsa cewa mijinta ne ya aike ta Kaduna ta karbo kudin wurin yan bindiga
  • Kakakin yan sandan jihar Katsina ya ce mijinta matar, Nura Murnai, shima dan bindiga amma yanzu ya tsere

Katsina, Katsina - Yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Hoton Matar Ɗan Bindigan Katsina Da Aka Kama Da Tsabar Kuɗi N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta
Aisha Nura, Matar Dan Bindigan Katsina da aka kama da N2.4. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Hoton Matar Ɗan Bindigan Katsina Da Aka Kama Da Tsabar Kuɗi N2.4m, Mijin Ya Tsere
Kudaden da aka kama tare da matar dan bindiga a Katsina. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

A cewar rahoton The Punch, ya ce Aisha yayin da ake mata tambayoyi ta bayyana cewa mijinta, wani Nura Murnai, ne ya aike ta ta karbo kudin daga hannun wasu yan bindiga a dajin Kaduna.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce mijinta, wanda a yanzu ya tsere, shima dan bindiga ne wanda ke tare da tawagar wani shugaban yan bindiga mai suna Abu Radda.

Matar da aka kama ta amsa cewa tabbas an kama ta da kudin

Aisha, yayin wani gajeren hira da aka yi da ita tare da manema labarai a hedkwatan yan sanda a Katsina ta amsa cewa a hannunta aka samu kudaden.

Ta yi magana cikin harshen hausa ta ce:

"Da gaske ne a hannu na aka samu kudin kuma miji na ne ya aike ni in karbo daga Kaduna."

Dogo Nabajallah: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan Katsina Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Rikicin Neman Aure

Kara karanta wannan

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullun

A wani labarin daban, rikici ya barke tsakanin bangarorin ƴan bindiga biyu masu adawa da juna a Katsina wadda ya yi sanadin mutuwar shugaban yan bindiga, Nabajallah, da wasu yan bindigan uku, rahoton The Punch.

Majiyoyi sun ce an kashe shugaban yan bindiga, Dogo Nabajallah a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa a ranar Laraba.

A cewar rahoton Premium Times Hausa wasu ƴan bindigan da ke adawa da shi ne suka afka masa suka kashe shi saboda rikicin neman aure da ke tsakanin yaronsa da bangaren su yan adawan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel