Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

  • Ministan yada labarai ya bayyana cewa, ba addinai ne matsalar Najeriya ba a yanzu
  • Ya bayyana yadda ake samun fahimtar juna tsakanin musulmai da kirista a Najeriya
  • Ya kuma ce, a yanzu wasu shugabannin addinai na kokarin tunzura mutane a kasar

Abuja - Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce wasu mutane a Najeriya na kokarin wargaza kasar saboda dalilai na son kai.

Premium Times ta ruwaito cewa Mohammed yayi wannan bayani ne a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli, a Abuja a taron gabatar da wani littafi.

Ya yi zargin cewa wasu abubuwa na kokarin kara tabarbarewar rikicin kabilanci da bambancin addini a Najeriya.

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya
Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce kalubalen da kasar ke fuskanta ba na kabilanci ko addini bane.

Ministan ya tuna cewa ya yi amfani da harabar Cocin Katolika na St Andrews dake Oro na garinsu don laccocin watan Ramadan tsawon shekaru uku a jere.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

A cewarsa, wannan babban misali ne na jituwa da addini da kuma zaman lafiya a Najeriya.

Ya ce:

“Na tsawon shekaru uku, wana Coci na ba da harabarta kyauta ga laccar watan Ramadan ta shekara-shekara.
"Wannan ya saba wa son kai da shakku da yawancin shugabannin addinai ke yadawa a yau."

Mohammed ya kuma bayyana cewa wani Coci a yankin Ikeja da ke cikin jihar Legas dole ya sauya hidimarsa na ranar Lahadi don ba Musulmai damar murnar Sallah lokacin da ranar ta fado a ranar Lahadi.

Sarki a arewacin Najeriya ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar jiharsa

Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna jihar kan su bar dazuzzukan fadin jihar ko kuma a tilasta musu yin hakan.

Gidan talabijin na Channels ta ce, Sarkin ya bayar da wa'adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi. Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa.

Kara karanta wannan

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifuka a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.

Kara karanta wannan

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Asali: Legit.ng

Online view pixel