Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura
- Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya ce Najeriya ta yi sa’ar samun Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin jagora a irin wannan lokaci
- A cewarsa ba don Buhari ne ke a kan mulki ba a yanzu, da 'yan Najeriya sun shiga mawuyacin hali
- Basaraken ya kuma yi kira ga shugaban kasar da ya jajirce waen kare kasar
Mai martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya ce Najeriya ta yi sa’a da samun Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a irin wannan lokaci.
Basaraken ya ce abubuwa "da sun kasance da wahala matuka" idan da a ce ba Buhari ba ne yake jan ragamar mulkin kasar.
Ya yi magana ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, lokacin da shugaban kasar ya ziyarce shi a fadarsa da ke Daura, jihar Kastina, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sarkin ya ce:
"Zuwanka Daura ya nuna kyawawan halayenka wanda muke matukar alfahari da shi.
“Ina iya baka tabbacin cewa maza, mata, yara, ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu a koyaushe suna farin cikin karbar ka kuma zasu yi muka addu’a.
“Yau ba ranar jawabai bane illa ranar godiya. Mun sami albarkatu sosai a matsayinmu na al'umma saboda kai ne shugaban ƙasar. Ka kawo daukaka ga yankinmu.
“A matsayinmu na al’umma, mun amfana sosai da yawan zirga-zirgar mutane da kungiyoyi da ke zuwa don taimaka mana a nan. Mun san saboda kai ne.
“Najeriya ta yi sa’ar samunka a wannan lokaci. Ba wai ina fadan hakan ne don in faranta maka rai ba, amma da ba ka kasance a kan karagar mulki ba da hakan zai yi wuya. Ina shakka idan za mu kasance a nan a yau.”
Sarkin ya ce dole ne shugaban kasar ya ci gaba da mai da hankali kan samun sakamako, musamman wajen kare kasar, jaridar The Cable ta ruwaito.
Bana Bukatar Ko Sisin Kobo Daga Hannunku, Shugaba Buhari Ga Yan Kwangila
A gefe guda, shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga waɗanda suka amfana da kwangilar gwamnati da su maida hankali wajen abinda a ka sa su, maimakon su dinga kokarin kaiwa wasu ɗai-ɗaikun jami'an gwamnayi kyaututtuka, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Buhari yayi wannan jawabin ne a Daura, jihar Katsina, ranar Jumu'a yayin da ya ziyarci Sarkin Daura, Dr. Umar Faruk Umar.
Buhari yace: "Bana bukatar ko naira daga hannunku, kuje ku tallafawa jama'an yankin ku maimakon ku zo kuna baiwa wasu ma'aikatan gwamnati."
Asali: Legit.ng