Gwamnatin Ganduje Ta Maida Martani Kan Shirin Hana Mata Tukin Mota a Ƙano

Gwamnatin Ganduje Ta Maida Martani Kan Shirin Hana Mata Tukin Mota a Ƙano

  • Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahoton dake yawo cewa ta na shirin kafa dokar hana mata tukin mota a jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis
  • Yace jita-jitar ba ta da tushe ballantana makama, kuma gwamnati ba zata zartar da abinda ya shafi al'umma a sirrance ba

Kano:- Gwamnatin jihar Kano, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa babu wani shiri na hana mata tukin mota a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Garba, shine ya faɗi haka yayin da yake martani kan jita-jitar dake yawo cewa gwamnatin jihar na shirye-shiryen kafa dokar hana mata tuki.

Garba ya bayyana labarin a matsayin karya tsagwaronta, inda ya ƙara da cewa gwamnatin Kano ba ta taba kawo makamancin wannan maganar ba.

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnatin Ganduje Ta Maida Martani Kan Shirin Hana Mata Tukin Mota a Ƙano Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Menene asalin labarin?

A jawabin kwamishinan, yace:

"Rahoton ba shi da tushe ballantana makama, kuma ba wani abu bane illa tunanin wasu mawallafa."

Kara karanta wannan

Gwamna Al-Makura ya karya jita-jitan cewa EFCC ta kame shi da matarsa, ya yi bayani

"Labarin dake yawo ba shi da wani tsayayyen tushe shiyasa ake danganta shi ga majiyar da babu ita."

Garba ya ƙara da cewa idan ma akwai wannan shirin, to gwamnatin Kano ba zata gudanar da taron sirri ba kuma ta zartar da abinda ya shafi jama'arta.

Channels tv ta rahoto kwamishinan yana cewa ƙasar Saudiyya da take da makamanciyar wannan dokar na tsawon lokaci, daga baya ta cire ta a shekarar 2018.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ji daɗin yadda wasu malamai suka fito suka kore wannan rahoton kuma suka nisanta kansu da lamarin.

A wani labarin kuma JAMB Ta Sake Shirya Jarabawar UTME 2021 Ga Wasu Dalibai, Ta Fadi Rana

Hukumar JAMB ta sake shiryawa ɗalibai sama da 18,000 jarabawar share fagen shiga manyan makarantu UTME saboda wasu matsaloli da suka samu.

Punch ta ruwaito cewa JAMB ta ɗau wannan matakin ne ga ɗaliban da suka samu matsalar zanen yatsa da kuma waɗanda jarabawar ta haɗe musu da NABTEB.

Kara karanta wannan

Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel