Hotunan Sheikh Ibrahim Zakzaky Ba Tare da Jami'an Tsaro ba Karon Farko Cikin Shekaru 6
- A karon farko cikin shekaru shida, mutane sun hangi shugaban mabiya akidar shi'a, sheikh Zakzaky ba tare da jami'an tsaro ba
- A ranar Laraba da ta gabata ne babbar kotu dake Kaduna ta wanke shehin malamin daga zargin da ake masa
- An dai hangi Zakzaky tare da wasu mabiyansa a filin sauka da tashin jiragen sama dake garin Kaduna ranar Alhamis da yamma
Kaduna:- A ranar Alhamis an hangi Shugaban kungiyar mabiya aƙidar shi'a (IMN), sheikh Ibrahim El-zakzaky ba tare da jami'an tsaron gidan yari ba karon farko cikin shekaru 6, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
A cikin tsawon shekaru shida da suka gabata, jami'an tsaro ne suke gadin sheikh Zakzaky zuwa duk inda za'a kaishi ko zai je.
Amma lokacin da aka hange shi a filin sauka da tashin jirage dake Kaduna ranar Alhamis da yamma, an ganshi tare da wasu mabiyansa Kuma ba tare da rakiyar jami'an tsaro ɗauke da bindigu ba.
Shehin malamin wanda babbar kotun Kaduna ta wanke shi daga zargin da ake masa ranar Laraba, ya kama hanya ne zuwa Abuja.
Sojoji sun damke malamin ne tun a shekarar 2015 bayan wata a rangama da ta faru tsakanin mabiyansa da jami'an sojin ƙasa a Zaria.
Hotunan Zakzaky babu jami'an tsaro
Wasu tsagerun yan bindiga sun gamu da ajalinsu
A wani labari na daban kuma, wasu tsagerun yan bindiga sun gamu da ajalinsu a jihar Sokoto yayin da suka sace wata mace mai ciki
Dakarun sojojin ƙasa na operation Hadarin Daji ne suka dirar wa yan bindiga inda suka harbe su har lahira. Dakarun sojojin sun kwato makami da suka hada da bindigu, mashin, motoci da sauransu
Daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar tsaro, Benard Onyeuko, shine ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar tsaro dake Abuja .
Asali: Legit.ng