Mailafia: Hana saida wa ‘yan canji Dalar Amurka zai kara rugurguza darajar Naira a Najeriya

Mailafia: Hana saida wa ‘yan canji Dalar Amurka zai kara rugurguza darajar Naira a Najeriya

  • Tsohon mataimakin gwamnan CBN ya soki haramtawa saida wa ‘yan kasuwa Dala
  • Obadiah Mailafia ya ce hana Bureau De Change kudin ketare waje zai iya taba Naira
  • Masanin tattalin arzikin ya na tunani za a fara fama da karancin kudin kasar waje

Abuja - Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Obadiah Mailafia, ya ce hana ‘yan canji kudin kasar waje ba zai taimaka ba.

Obadiah Mailafia ya soki sabon tsarin CBN

The Cable ta rahoto Obadiah Mailafia ya na cewa matakin da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya dauka zai karya darajar Naira.

Da yake hira da Punch, Mista Obadiah Mailafia yace ya kamata CBN su yi hattara domin haramta wa ‘yan canji samun dala zai iya ruguguza kudin gida.

Mailafia wanda ya rike mataimakin gwamna a bankin CBN yace za a samu karancin kudin kasar waje saboda sharudan da bankuna za su fito da shi.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

“Idan ba mu yi hattara ba, wannan mataki zai iya jawo darajar Naira ta tabarbare saboda za ka iya samun kudin kasar waje a minti biyar a hannun ‘yan canji.”
“’Yan BDC za su saurare ka, amma idan ka je bankin da ya fi kusa da kai, za ka yi ta bin layi ne.”

Bankin CBN
Babban bankin kasa na CBN
Asali: Facebook

“CBN ba su fada mana farashi ba, banki za su ci riba da farashin da aka yanke. Ba mu san ko kazamar riba za su nemi su samu ba, ko za su yi sauki.”
“Bankuna sun fi kowa dabarar cin kudi. Sun saba da haka, ba na tunanin za su canza halinsu.”

A ra’ayin Mailafia, za a zo lokacin da ake wahalar kudin waje, sai farashi ya karu a kasuwa saboda karancin da ake fama da shi, daga nan sai Naira ta ruguje.

Masanin tattalin arzikin ya ce ba za a iya amince wa bankuna saida wa jama’a kudin kasar waje ba domin za su sa farashin Naira ya kara yin kasa sosai.

Kara karanta wannan

Osinbajo:Gwamnatin Buhari ta hada-kai da UNICEF, a koyawa mutum miliyan 20 neman na-kai

Naira ta doshi N520 a kasuwar canji

A makon nan ne aka ji cewa darajar Naira ta dada fadi bayan sanarwar CBN na daina sayar wa 'yan kasuwar canji Dalar Amurka da kudin kasashen waje.

Jim kadan bayan sanarwar da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele ya bada na dakatar da sayar da Dala ga 'yan canji, farashin Dalar ya lula har N520.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel