Osinbajo: Gwamnatin Buhari ta hada-kai da UNICEF, a koyawa mutum miliyan 20 neman na-kai

Osinbajo: Gwamnatin Buhari ta hada-kai da UNICEF, a koyawa mutum miliyan 20 neman na-kai

  • Gwamnatin Najeriya za ta hada-kai da UNICEF domin a koyawa miliyoyin mutane abin yi
  • Kamfanin Generation Unlimited (GenU) ne zai horar da matasa a karkashin shirin UNICEF

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya da na jihohi suna hada-kai da wani kamfani da nufin a samar wa mutane ayyukan yi.

GenU za ta taimaka wa matasa da mata a Najeriya

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati za ta shiga yarjejeniya da kamfanin Generation Unlimited Nigeria domin ta koya wa mutane aikin da zai iya rike su.

This Day ta rahoto mataimakin shugaban Najeriyar ya na cewa wadanda za a koya wa wannan aiki za su samu na-abinci da damar sun cin ma burinsu a rayuwa.

Generation Unlimited (GenU), wani shiri ne da kungiyar tallafa wa yara na majalisar dinkin Duniya watau UNICEF, da aka kaddamar a Satumban 2018.

Wajen kaddamar da shirin, Osinbajo ya ce tsarin zai taimaka ta hanyoyi uku; koyar da ayyukan kafafen zamani, ba matasa aiki da koya masu shiga mutane.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Kamfanin na GenU Nigeria zai bada muhimmanci sosai wajen koya wa mata neman kudi a Najeriya.

Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Mutane miliyan 20 ake sa rai za su amfana a kasar nan

“Zai ba mutane miliyan 20 aikin yi a Najeriya, ya sada su da yadda za su samu kudi, da hanyoyin samun na-kashewa, ya taimaka masu wajen cinma burinsu.”

Osinbajo ya ce an tsara shirin ne ta yadda zai hada matasa biliyan daya da sababbin dabaru da shirye-shirye iri-iri a kasashe 40 da ke cikin nahiyoyi shida.

Jaridar ta rahoto mataimakin shugaban kasar ya na cewa akwai dinbin masu taso wa a Najeriya, inda ya ce rashin koya wa wadannan yara sana’a, hadari ne.

“Fadar shugaban kasa, ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma jihohi, za su hada-kai da Generation Unlimited Nigeria, da kasashen waje, domin kai ga ci.”

Shugaban gidauniyar Tony Elumelu Foundation da na kamfanin GenU Nigerian sun yi jawabi a taron, su ka bayyana muhimmancin horas da matasan kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Buhari za ta kammala aikin da aka yi shekaru 42 ana jira a Najeriya

A makon nan ne aka ji cewa malaman jami’a a karkashin kungiyar ASUU, suna yi wa gwamnatin tarayya barazanar cigaba da yajin-aikin da suka janye a 2020.

A 2020, sai da kungiyar ASUU ta shafe wata da watanni ba ta koyar da ‘dalibai ba. ASUU ta ce gwamnatin tarayya ba ta cika duk alkawuran da ta dauka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng