Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Kutsa Ma'aikatar Gwamnati a Nasarawa, Sun Sace Tsabar Kuɗi Naira Miliyan 100
- Yan bindiga da ake zargin yan fashi ne sun sace Naira miliyan 100 daga ma'aikatar kudi na jihar Nasarawa
- Yan bindigan sun bi sahun ma'aikatan ne da suka tafi wani banki a Lafia suka ciro kudin don a biya kananan ma'aikata
- Kwamishinan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na jihar, Mr Haruna Ogbole ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce ana bincike
Lafiya, Jihar Nasarawa - Yan bindiga da ake kyautata zaton yan fashi ne, a ranar Alhamis, sun kai hari Ma'aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na jihar Nasarawa sun sace Naira miliyan 100, Daily Trust ta ruwaito.
Ofishin na kusa da ofishin babban akanta janar na jihar, inda aka ajiye jami'an tsaro na NSCDC da yan sanda domin samar da tsaro.
Sai dai, ba su samu nasarar hana satar ba.
Ta yaya yan bindigan suka sace kudin?
Wani ganau, wanda ya nemi a boye sunansa ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa yan fashin sun bi bayan jami'an ma'aikatar ne bayan sun tafi wani banki a Lafiya sun ciro kudi da za a biya kananan ma'aikata.
Ganau din ya ce:
"A cikin harabar ma'aikatan ne yan bindigan suka kwace N100m daga hannun jami'an ma'aikatar da ke kokarin ciro kudin daga motar da ta kawo kudin dakin ajiyar kudi na ma'aikatan.
"Yayin kwace kudin, yan bindigan sunyi ta harbi sama hakan yasa ma'aikatan hukumar suka kwanta kasa su kuma yan bindigan suka kwace N100m cikin sauki."
Ya ce yan bindigan sun yi nasarar sace kudin ne domin ma'aikatar bata dauki jami'an tsaro da za su basu kariya tare da kudin ba.
Kwamishinan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na jihar, Mr Haruna Ogbole, wanda ya tabbatar da fashin ta hirar wayar tarho, ya ce ana bincike kan lamarin.
EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa
A wani labarin, mun kawo muku cewa Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami'an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.
Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.
Asali: Legit.ng