Da Duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da wani sashen jami'ar ATBU ta Bauchi
- Gobara ta yi kaca-kaca da wani yanki a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi
- Rahotanni sun ce, takardu masu muhimmanci da dama sun kone, amma dai babu asarar rai
- Har yanzu hukumar makarantar bata ce komai game da wannan mummunan yanayin da ya faru ba
Wata gobara da ta tashi ta yi kaca-kaca tare da lalata wani bangare na sashen Kimiyyar Noma a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) ta Bauchi.
A cewar wata majiya, lamarin ya faru ne a harabar din-din-din ta jami’ar da ke Gubi a kan hanyar Kano, da misalin karfe 8 na daren Laraba.
Legit Hausa ta samu daga jaridar Vanguard, wacce ta samu labarin cewa dalibai da sauran wadanda ke kusa da yankin sun tsere domin kare lafiya yayin da ake kokarin shawo kan wutar daga yaduwa zuwa wasu sassan Jami'ar.
Har yanzu dai ba a samu labarin asarar rayukan mutane ba, amma wasu majiyoyi sun ce babu wani rahoto game da asarar rayuka sakamakon gobarar.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wani bayani a hukumance daga Jami'ar.
Wata majiya daga Jami’ar ta bayyana cewa gobarar ta faru ne lokacin da kusan babu kowa a cikin ginin, lamarin da ya rage yiwuwar asarar rayuka amma ta ce takardu masu mahimmanci da sauran kayayyaki sun lalace sakamakon gobarar, Tribune Online ta ruwaito.
Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi
Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin doka da aka don bai wa ma’aikatan hukumar kashe gobara ta tarayya makamai, Channels Tv ta ruwaito.
Kudirin an mika shi ne don bai wa 'yan kwana-kwana ikon daukar makamai don kare su daga hare-haren jama'a yayin da suke kan ayyukansu.
'Yan majalisar sun cire kudirin ne ta hanyar kin amincewa da kudirin da Wakili Thomas Ereyitomi ya gabatar.
Gwamnatin Buhari za ta samar wa ma'aikatan kashe gobara bindiga, ta fadi dalili
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kirkiro wani bangare a hukumar kashe gobara wacce za ta ba da damar daukar makami don samar da bindigogi ga ma'aikatan kashe gobara yayin gudanar da ayyukansu.
Wannan ya biyo bayan yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi na magance kalubalen da galibin ma’aikatan kashe gobara ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu, ta fuskar harin tsageru da masu barnatar da kadarori a wuraren gobara a fadin kasar.
Daraktan yada labarai na ma’aikatar cikin gida, Misis Blessing Lere-Adams, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Abuja.
Asali: Legit.ng