Bishop Kuka yayi kira ga shugabannin Najeriya da su daina daukar rantsuwar da basu kiyayewa
- Mathew Hassan Kukah ya caccaki masu kujerun siyasa a Najeriya dake daukan rantsuwa da ba zasu iya cikawa ba
- Babban limamin cocin katolikan na Sokoto, ya bada wata sabuwar rantsuwa da ya dace 'yan siyasa su dauka
- Ya sanar da hakan ne yayin da ya halarci jana'izar Rabaren Alphonsus, wanda 'yan bindiga suka kashe a jihar Katsina
Mathew Hassan Kuka, babban limamim cocin katolika na jihar sokoto, ya jajanta yadda shugabannin siyasa ke rantsuwa da kuma yadda rashin tsaro ke hauhawa a kasar nan.
Ya bukaci 'yan siyasa da su daina daukan rantsuwar da ba zasu iya cikawa ba, HumAngle ta ruwaito.
Bishop Kuka ya sanar da hakan ne a Kaduna, ranar Talata, 1 ga watan Yunin 2021 yayin bikin birne marigayi Rabaren Alphonsus Yashim Bello, limamin cocin katolika na Katsina wanda 'yan ta'adda suka kashe a ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021.
"Wannan mummunan dabi'a ta yankawa tare da kashe mutanen da basu da laifin zaune ko na tsaye na nuna cewa kyakyawar fadar shugaban kasanmu, majalisar dattawa, kyawawan gidajen gwamnatocinmu, jiragenmu da sauransu ba alamu bane na wayewa saboda mun yi nisa daga wayewa," Kukah yace.
KU KARANTA: JTF ta kama mutum 10 da ake zargi da kisan jami'an tsaro a Akwa Ibom, an samu miyagun makamai
KU KARANTA: Har yanzu gwamnati bata tuntubemu ba, Hukumar makarantar da aka sace yara156
A yayin cigaba, Kukah ya bada shawarar cewa masu mukaman siyasa sun dinga daukan rantsuwa kamar haka: "'Yan kasa, ku ji da kanku. Tsaronku na hannunku. Baku kariya ba shine a gabanmu ba. 'Yan bindiga zasu iya zuwa su kashe ku a lokacin da suka so, su yi muku fyade, sata, garkuwa da ku tare da kashe ku."
"'Yan bindigan zasu iya shafe yankunanku, lalata gidajenku, barnata gonakinku da kadarorinku. Zasu iya garkuwa ko kashe 'ya'yanku a lokacin da suka so. Zasu iya sace shanunku. Idan sun sace 'ya'yanku, matanku ko mazanku, zamu kira ku da 'yan ta'adda saboda kun basu kudin fansa kuma na sako su."
"Muna shirya dokoki da zasu kai ku gidan yari na shekaru 15 a kan wannan laifin da kuka yi wa kasarku ta gado."
"Ba mu baku damar sasanci ko cinikayya da 'yan bindiga ba. Kada ku wahalar da kanku wurin sanar damu an sace muku masoyanku. Kada ku yi tsammanin zamu halarci jana'izarsu. Idan zaku sanar damu mutum nawa aka kashe ko aka yi garkuwa dasu a yankunan, dole ne ku zo Abuja ko kuma babban birnin jiharku."
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya tace ta bankado wani wurin hada bindigogi AK-47 a karamar hukumar Jos ta kudu dake jihar Filato a ranar Laraba.
Mai magana da yawun rundunar, CP Frank Mba a Abuja yace sun cafke wasu mutane biyu masu matsakaitan shekaru masu suna Joe Michael da Iliya Bulus a kan laifin mallakar wurin tare da wasu wadanda ake zargi har 79.
Wadanda ake zargin kamar yadda Mba yace, an kama su da taimakon rundunar IRT da ta STS na hukumar 'yan sandan, The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng