'Wannan na shan ruwa ne': Ƴan bindiga da suka sace mai AZECO Pharmacy sun ƙi karɓar N10m, sun ce N30m suke so

'Wannan na shan ruwa ne': Ƴan bindiga da suka sace mai AZECO Pharmacy sun ƙi karɓar N10m, sun ce N30m suke so

  • Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da shugaban AZECO Pharmacy, Abdulazeez Obajimoh sun ki karbar N10m
  • Masu garkuwar sun raina kuɗin fansar suna mai cewa abin da aka basu 'canji ne na shan ruwa' don haka a biya su N30m
  • Shugaban kungiyar ƙwararrun masana magunguna na Nigeria, PSN, reshen jihar Kogi ya yi kira ga gwamnatin jihar da jami'an tsaro su magance matsalar garkuwa

Okene, Jihar Kogi - Masu garkuwa da suka sace shugaban AZECO Pharmacy a Okene, jihar Kogi, Abdulazeez Obajimoh, sun ki karbar N10m da iyalansa suka bayar, sun ce N30m za a biya kafin su sako shi, The Punch ta ruwaito.

Tun a farkon watan Yuli ne masu garkuwar suka sace Obajimoh a garin Iruvucheba a ƙaramar hukumar Okene ta jihar Kogi.

'Wannan na shan ruwa ne': Ƴan bindiga da suka sace mai AZECO Pharmacy sun ƙi karɓar N10m, sun ce N30m suke so
Taswirar Jihar Kogi: Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A cewar wani daga iyalansa, masu garkuwar sun kira a ranar Alhamis sun ce ba za su ƙarba Naira miliyan 10 da iyalansa suka bada ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

Majiyar, a cewar rahoton The Punch ta ce masu garkuwar sun ce abin da aka bada 'canji ne kawai na shan ruwa' don haka suka nemi a biya su Naira miliyan 30.

Kungiyar PSN ta yi kira ga gwamnatin Kogi da jami'an tsaro su dakile garkuwa da mutane

Kungiyar ƙwararrun masanna magunguna ta Nigeria, PSN, reshen jihar Kogi, ta koka kan yadda ake yawan kaiwa mambobin ta hari da sace su a jihar.

Shugaban PSN na jihar Kogi, Dr Lawal Muhammad, cikin wata sanarwa, ya ce mafi yawancin kudin da ake mambobin kungiyar ke hada-hada ta shi bashi ne daga bankuna.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da jami'an tsaro su yi haɓɓasa domin ganin sun kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane.

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin mai kama da wannan, Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta ce maza su hakura kawai, a mika wa mata ragamar Najeriya

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel