Dakarun Soji Sun Damke Mutum 19 Dake Tallafawa Yan Bindiga a Jihar Zamfara
- Jami'an sojin ƙasa sun samu nasarar kama mutum 19 dake tallafawa yan bindiga a Zamfara
- An kama mutanen ne da laifin bada bayani domin a sace wani ko kuma suce a kashe wani a ƙauyen Ɗansadau
- Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa mutanen da aka kama sanannu ne kuma na kwarai
Rundunar sojin Operation hadarin daji sun damke mutum 19 da ake zargin suna haɗa kai da yan binidga a Ɗansadau ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
An kama waɗanda ake zargin saboda suna da alaƙa da ayyukan yan bindiga da kuma garkuwa da mutane a yankin, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Da yake tabbatar da kame mutanen, wani mazaunin yankin, Mallam Nuhu Dansadau, yace kama mutanen yayi matuƙar baiwa mutane mamaki domin waɗanda ake zargin kowa ya sansu.
Nuhu ya ƙara da cewa mazauna ƙauyen Ɗansadau na cikin murna da farin ciki game da kame mutanen, yace:
"Muna cikin farin ciki kuma munyi mamaki sosai saboda mafi yawancin su sanannu ne, gasu shiru-shiru, masu kirki, amma ashe waɗanda bamu tsammani ne."
Dukan mutanen sanannu ne
Ya bayyana cewa mafi yawancin su an kama su ne saboda suna umartar yan bindiga su sace wane ko su kashe wane.
"Wasu daga cikinsu an cafke su ne da zargin bada bayanin mutane a yi garkuwa da su ko a kashe su." inji shi.
Shugaban yan bindiga ya kira mai gari
Nuhu yace shugaban yan bindigan dake yankin ya kira magajin garin Dansadau ta wayar salula yana tambayarsa me yasa ake kame mutane a yankin.
A cewar Mallam Nuhu tun bayan da aka kama mutanen yan bindiga sun zagaye ƙauyen suna kokarin kai wa mutane hari.
Yace a halin yanzun yan garin Ɗansadau ba sa iya bacci da idanunsu a kulle saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.
Asali: Legit.ng