Ku Kawo Nnamdi Kanu Kotu Idan Ba Kashe Shi Kuka Yi Ba, IPOB Ta Faɗa Wa DSS

Ku Kawo Nnamdi Kanu Kotu Idan Ba Kashe Shi Kuka Yi Ba, IPOB Ta Faɗa Wa DSS

  • Kungiyar IPOB ta nuna damuwar ta game da halin da shugabanta Nnamdi Kanu ke ciki
  • IPOB ta ce hanya guda da za ta tabbatar shugabanta na da rai shine a kawo shi kotu
  • DSS ba ta kawo Nnamdi Kanu kotu ba a ranar Litinin hakan yasa alkali ta sake dage sauraron shari'ar

Kungiyar masu fafutikan kafa kasar Biafra, IPOB, ta bayyana bacin ranta game da rashin kawo shugabanta Nnamdi Kanu kotu da gwamnatin tarayya ta yi a ranar Litinin a Abuja, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta ce hakan shiri ne da gangan domin kara azabtar da shugabanta da kuma alama da ke nuna cewa akwai yiwuwar ba shi da cikakken lafiya.

Ku Kawo Nnamdi Kanu Kotu Idan Ba Kashe Shi Kuka Yi Ba, IPOB Ta Faɗa Wa DSS
Mazi Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Sanarwar da IPOB ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaran ta, Emma Powerful, ta ce hanya guda tilo da za a tabbatarwa kungiyar shugabanta na nan da rai shine kawo shi kotu.

Kara karanta wannan

Hatta Musa Ya Yi Hijira Saboda Fir'auna, Babu Laifi Don Igboho Ya Tsere, Afenifere

Kungiyar ta kuma bukaci a saki wadanda aka kama a Abuja da wasu sassan kasar saboda nuna goyon baya ga shugabansu, Kanu a cewar rahoton na The Nation.

Sanarwar ta ce:

"Akwai yiwuwar an kashe shugaban mu duba da cewa bashi da lafiya tun da aka sace shi sannan DSS ta ki amincewa likitocinsa na kansa su duba shi.
"DSS ta nuna cewa abin da muke zargi ba gaskiya bane ta hanyar kawo shi kotu ko su bar lauyoyinsa da iyalansa su gana da shi. An kusa kure mu. Kada Nigeria ta raina IPOB. Ba zamu yarda shugaban mu ya mutu a tsare ba.
"Muna mika godiyar mu ga dukkan kasuwani, bankuna, hukumomin gwamnati, tashoshin mota da kamfanonin sufuri da sauransu da suka nuna goyon baya ga shugaban mu Mazi Nnamdi Kanu ba tare da sanarwa a hukumance ba.
"Muna godiya ga dukkan yan Biafra da abokan Biafra da suka nuna goyon baya ga shugaban mu a yau."

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel