Abin Da Yasa Buhari Ke Tsallake Likitocin Nigeria Ya Tafi Landan Duba Lafiyarsa, Adesina

Abin Da Yasa Buhari Ke Tsallake Likitocin Nigeria Ya Tafi Landan Duba Lafiyarsa, Adesina

  • Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa Buhari ya gwammace ya rika zuwa Landan duba lafiyarsa
  • A cewar Adesina, likitocin da Buhari ke zuwa gani a can sune ke da bayannan lafiyarsa don haka ya ke tafiya can din
  • Hadimin na shugaban kasa ya ce tun kimanin shekaru 40 da suka gabata Buhari ke tare da likitocinsa na Burtaniya don haka ya fi dacewa ya cigaba da zuwa can

Mashawarci na musamman ga Shugaban Kasa kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina, ya ce mai gidansa ya fi son zuwa Birtaniya a duba lafiyarsa ne don likitocin Nigeria ba su da bayansa na lafiya, The Punch ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa Adesina ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa Buhari ba ya yarda likitoci su duba shi a Nigeria yayin wani shiri a gidan talabin na Channels Television.

Shugaba Muhammadu Buhari
Abin Da Yasa Buhari Ke Tsallake Likitocin Nigeria Ya Tafi Landan Duba Lafiyarsa, Adesina. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

A cewarsa, likitocin Burtaniya ne kadai suka da bayanan lafiyar Buhari.

Fiye da shekaru 40 dama likitocin Burtaniya ke duba Buhari, Adesina

Ya kara da cewa tun kimanin shekaru 40 da suka gabata likitocin na Burtaniya ne da duba lafiyar shugaban kasan.

Ya ce:

"Shugaban kasar ya dade tare da likitoci da tawagar masu kulawa da lafiyarsa fiye da shekaru 40.
"Abin da ya fi dacewa shine ya cigaba da wadanda suka san bayannan lafiyarsa shi yasa ya ke zuwa Landan don ganinsu. Su ke duba shi fiye da shekaru 40 da suka shude. Idan za ka iya biya, toh ka cigaba da zuwa wurin wadanda ke da bayyanan lafiyarka."

Legit.ng ta ruwaito cewa Buhari ya tafi Landan a ranar Litinin domin hallartar taron ilimi bayan nan kuma zai tafi likitocinsa su duba lafiyarsa a cewar fadar shugaban kasa.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel