Dalilin da yasa Buhari ke zuwa Landan ganin Likita, Femi Adesina

Dalilin da yasa Buhari ke zuwa Landan ganin Likita, Femi Adesina

  • Idan mutum na da kudin zuwa, kawai ya tafi, cewar Femi Adesina kan zuwan Buhari Ingila
  • Ya kare zuwan da maigidansa ke yi Birtaniya kowani shekara
  • Jam'iyyar PDP tayi Alla-wadai da zuwa neman lafiyan da Buhari keyi zuwa kasar waje

Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana dalilin da yasa maigidansa ke zuwa kasar Birtaniya neman lafiya tun da ya hau mulki.

Jawabi yayin hira a shirin Politics Today na tashar ChannelsTv, Adesina yace Buhari ya saba da zuwa Birtaniya tun shekaru 40 da suka gabata kuma akwai bukatar ya cigaba da hakan.

Yayinda aka tambayesa shin me zai hana Buhari ganin Likitocin Najeriya, Adesina yace:

"Shugaba Buhari ya kwashe shekaru 40 yana ganin wadannan Likitoci sama da shekaru 40."
"Akwai bukatar ya cigaba da ganin Likitocin da suka san lafiyarsa kuma wannan shine dalilin da yasa yake zuwa Landan ganinsu. Tunda akwai kudin, ya fi mutum ya cigaba da amfani da Likitocin da suka san lafiyarsa."

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Buhari Ke Tsallake Likitocin Nigeria Ya Tafi Landan Duba Lafiyarsa, Adesina

Dalilin da yasa Buhari ke zuwa Landan ganin Likita, Femi Adesina
Dalilin da yasa Buhari ke zuwa Landan ganin Likita, Femi Adesina Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Wa zai cigaba da jan ragamar mulki?

Yayinda aka tambayesa shin Buhari zai cigaba da jan ragamar mulki daga Birtaniya ne, yace idan bai dawo ba bayan makonni uku, mataimakinsa zai zama mukaddashi.

Yace:

"Abubuwa na cigaba da gudana a kasar, akwai mataimakin shugaban kasa da zai kula da su. Babu wani gibi."

Buhari ya dira Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Landan, kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa da kuma halartan taron kasa da kasa kan inganta ilimi a duniya.

Buhari ya isa Ingila da cikin dare a jirgin shugaban kasa Eagle001.

Ya samu kyakkyawan tarba daga Jakadan Najeriya dake Landan, Amb. Sarafa Ishola, da shugabar yankin Sussex, Mrs Jennifer Tolhurst, da kuma Mr David Pearey.

Shugaban kasa zai kwashe yan kwanaki domin ganin Likitansa da ya kamata ace ya gani tun a baya. Zai dawo Najeriya a tsakiyar Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng