Shugaba Buhari Ya Aike da Sakon Taya Murna Ga Gwamna Bayan Kotun Koli Ta Yanke Hukunci

Shugaba Buhari Ya Aike da Sakon Taya Murna Ga Gwamna Bayan Kotun Koli Ta Yanke Hukunci

  • Shugaba Buhari ya taya gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, murnar samun nasara a kotun koli
  • Buhari yace wannan nasarar ta kara nuna karfin da jam'iyyar APC ke da shi da kuma damar sake ɗarewa mulki nan gaba
  • Shugaban ya yi kira ga waɗanda ke ɓangaren adawa su aje makamansu domin kawo cigaba a jihar Ondo

FCT Abuja:- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya gwamna Rotimi Akeredolu, na jihar Ondo murna bisa nasarar da ya samu a kotun koli, kamar yadda punch ta ruwaito.

Leadership ta ruwaito cewa kotun ta tabbatar nasarar sake zaɓen Akeredolu a zaɓen 10 ga watan Oktoba, 2020.

Buhari a sakon taya murna da mai taimaka masa, Femi Adesina, ya fitar ranar Laraba a Abuja ya roki gwamnan da sauran shugabannin jam'iyya a jihar da su sanya al'ummarsu a sahun farko a duk wani aiki ko shiri na cigaba da suka kirkiro.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari Ya Aike da Sakon Taya Murna Ga Gwamna Bayan Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Hoto: @Buharisallau
Asali: Instagram

Shugaban ya jaddada cewa jam'iyyar APC zata cigaba da dogara da ɗumbin ayyukan alherinta da kuma amincewar da masu zaɓe suka mata.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a

Buhari ya yabawa Gwamna Akeredolu

Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnan bisa namijin kokarin da yake yi wajen kawo cigaba a jihar Ondo.

Yace: "Saboda kokarin da kake yi a ɓangaren lafiya, ilimi, da tsaro ne ya sanya masu zuba hannun jari suke tururuwa jihar."

"Hukuncin kotun koli wanda ya biyo bayan na kotun ɗaukaka kara ya ƙara nuna karfi da matakin da jam'iyyar APC ta taka, da kuma damar da take da shi na lashe zaɓen dake tafe."

Hakanan kuma shugaba Buhari yayi kira ga yan adawa da su aje makamansu, su yi aiki domin cigaban jihar Ondo.

A wani labarin kuma Ku Yi Murabus Daga Mukamanku Ko Na Sallameku, Gwamna Ya Gargadi Makusantansa

Gwamna Douye Diri, ya gargaɗi yan majalisar zaratarwar jihar Bayelsa da su dakata da fara siyasar wuri

Gwamnan yacee duk wanda ya jefa kansa a cikin siyasar wuri ta 2023 ya janye ko gwamnati ta sallame shi.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262