Labari Da Ɗumi-Ɗumi: An Datse Kan Shugaban Ƙungiyar Ƴan Sa Kai a Rivers

Labari Da Ɗumi-Ɗumi: An Datse Kan Shugaban Ƙungiyar Ƴan Sa Kai a Rivers

  • Wasu miyagu da ake zargin yan kungiyar asiri ne sun datse kan tsohon shugaban kungiyar yan sa-kai ta OSPAC a Rivers
  • Yan bindigan sun halaka Alez Uwazurike ne a daren ranar Talata a garinsu na Umudioga karamar hukumae Emohua
  • Rundunar yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa ta tura jami'anta garin kuma abubuwa sun daidaita

Wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyar asiri ne sun kashe tare da datse kan kwamandan wata kungiya sa kai a garin Umudioga, ƙaramar hukumar Emohua na jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Alex Uwazurike, kafin rasuwarsa shine shugaban wata tsohuwar kungiyar sa kai mai suna OSPAC a garin na Umudioga.

Labari Da Ɗumi-Ɗumi: An Datse Kan Shugaban Ƙungiyar Ƴan Sa Kai a Rivers
Taswirar Jihar Rivers. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

An kashe shi ne a fagen ranar Talata a yayin da yan bindigan suka kutsa garin suka kashe shi suka datse jikinsa kuma suka ƙona shi.

Kara karanta wannan

An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto

Mai magana da yawun yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin yana mai cewa, "mun kwantar da tarzomar kuma mutanen mu suna can a unguwar."

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Darajar Naira ta fadi bayan sanarwan CBN na daina sayarwa yan kasuwar canji Dalar Amurka

Asali: Legit.ng

Online view pixel