Babban Sarki a Arewa Ya Roƙi Ƴan Bindiga Su Ƙyalle Manoma Su Koma Gonakinsu

Babban Sarki a Arewa Ya Roƙi Ƴan Bindiga Su Ƙyalle Manoma Su Koma Gonakinsu

  • Mai martaba Sarkin Kontagora Alhaji Sa'idu Namaska ya roki yan bindiga su kyalle monoma su koma gonakinsu
  • Sarkin ya ce muddin manoma ba su samu sun yi noma ba yunwa da fatara za ta munanan a kasar duba da cewa a bara ma ba a yi noma yadda ya kamata ba
  • A bangarenta, gwamnatin jihar Niger ta ce an fara samun saukin harin yan bindigan kuma gwamnati na iya kokarinta don samar da tsaro

Minna, Jihar Niger - Sarkin Kontagora, Alhaji Sa'idu Namaska ya roki yan bindiga su dena hare-hare su kyalle manoma su koma gonakinsu don kaucewa yunwa da karancin abinci duba da cewa daminan 2021 ta kama, News Wire NGR ta ruwaito.

Sarkin ya ce tun yanzu ana fama da karancin abinci saboda annobar korona da rashin tsaro sun shafi daminan 2020, yana mai cewa lamarin zai munana idan yan bindigan ba su bari manoma sun koma gona ba.

Babban Sarki a Arewa Ya Roƙi Ƴan Bindiga Su Ƙyalle Manoma Su Koma Gonakinsu
Mai Martba Sarkin Kontagora, Alhaji Sa'idu Namaska. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

Sarkin wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar manoman jihar Niger, AFAN, Alhaji Shehu Galadima ya yi wannan jawabin ne yayin taron baje kolin kayan noma karo na uku a Minna babban birnin jihar.

Sarkin ya kara da kira ga gwamnati ta karo sabbin jami'an tsaro na gonaki da za su tabbatar manoman sunyi aikinsu lafiya idan sun koma gonakinsu.

Abin da kwamishinan noma na Niger ya ce game da tsaro?

Kwamishinan noma na jihar Niger, Zakari Haliru Jikantoro a martaninsa ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar na iya kokarinta don ganin ta tsare kowanne mazaunin jihar.

A cewarsa, an fara samun saukin hare-haren yan bindiga a jihar saboda matakin da gwamnatin jihar ta dauka a baya-bayan nan.

Ya ce:

"Idan ka lura, an fara samun saukin hare-haren yan bindiga saboda matakan tsaro da gwamnatin jiha ta dauka don ganin yan bindigan ba su hana manoma aiki ba."

Dalilin shirya taron?

A kan taron baje koli na noman, Jikantoro ya ce ana sa ran yan kasuwa fiye da 100, jami'an gwamnati, masu ruwa da tsaki a bangaren noma za su hallarci taron na kwanaki biyu.

Ya ce an shirya taron ne manoma su samu sabbin iri da kayan aiki, karfafawa manoma biyan basusukan da suka ci, sada masu sayar da injinan noma da masu siya da bada shawarwari kan sabbin dabarun noma na zamani.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Asali: Legit.ng

Online view pixel