Da duminsa: An sheke DPO yayin da tsagerun IPOB suka kai farmaki Imo

Da duminsa: An sheke DPO yayin da tsagerun IPOB suka kai farmaki Imo

  • Miyagun 'yan bindiga da ake zargin tsagerun IPOB sun halaka CSP Fatmann Dooiyor
  • Gagararrun tsagerun sun tsinkayi garin a motocinsu uku inda suka fara tada tarzoma
  • 'Yan sandan sun tabbatar da sheka shida da aka yi kuma aka damke 11 daga cikinsu

Oru ta gabas, Imo

'Yan bindiga da ake zargin tsagerun IPOB ne sun sheke CSP Fatmann Dooiyor. Dooiyor wanda shine babban jami'in dan sanda a Omuma, garinsu Gwamna Hope Uzodimma dake karamar hukumar Oru ta gabas dake jihar Imo.

Gagararrun 'yan bindiga sun tsinkayi babbar kotun tarayya dake Abuja inda aka gurfanar da Nnamdi Kanu. Jami'an DSS basu kai shi kotu ba, lamarin da yasa aka dage shari'ar zuwa watan Oktoba, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

Da duminsa: An sheke DPO yayin da tsagerun IPOB suka kai farmaki Imo
Da duminsa: An sheke DPO yayin da tsagerun IPOB suka kai farmaki Imo
Asali: Original

KU KARANTA: Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

'Yan sanda sun sheke shida, sun cafke 11

Kamar yadda takardar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam ya fitar, yace 'yan sanda sun sheke shida daga cikin 'yan bindigan kuma an cafke 11 daga cikinsu.

Abattam ya ce tawagar 'yan bindiga sun bayyana a motoci uku wadanda suka kutsa yankin amma 'yan sanda da suka samu jagorancin ACP Benjamin Abang suka fatattakesu.

Ya ce an sanar da 'yan sanda tun lokacin da aka hango 'yan bindigan suna tafe a tawaga guda zuwa garin Omuma, Daily Trust ta ruwaito.

Abattam ya ce, "Rundunar 'yan sandan sun gaggauta daukan mataki kuma sun kaddamar da farmakin ba-zata kan 'yan bindigan wanda yayi sanadin sheka 'yan bindiga shida tare da cafke wasu 11.

"Amma cike da takaici, an yi rashin CSP Fatmann Dooiyor wanda ya rasa ransa yayin farmakin."

“'Yan sandan daga bisani sun samo motoci uku da 'yan bindigan suka tsere suka bari. Sun hada da motoci kirar Toyota Highlander SUV da lambar rijista Abia MBL 517 AT da LAGOS , JJJ 984 EL da kuma wata mai launin ruwan madara kirar Lexus Jeep.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu

"A halin yanzu tawagar 'yan sandan karkashin shugabancin ACP Evans E.Shem suna duba dajin domin bankado inda 'yan bindigan suka nufa," takardar tace.

Masu garkuwa da mutane sun fara karbar kudin fansa ta banki

Masu garkuwa da mutane dake barna a babban birnin tarayya (FCT) suna cigaba da habaka saboda sun fara karbar kudin fansa ta hanyar amfani da asusun bankunansu, Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da mutane har kashi biyu a yankin Tungan Maje dake wajen garin. Miyagun sun koma yankin a ranar Laraba bayan sun sace mutum 6 daga yankin.

Sauran yankunan babban birnin tarayya da suka hada da Kuje, Bwari da Abaji suna fuskantar hauhawar lamarin garkuwa da mutane a watanni kadan da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng