Gwamnatin Buhari ta gargadi mazauna waje kan daukar nauyin masu rikita Najeriya
- Gwamnatin Najeriya ta gargadi 'yan Najeriya mazauna kasashen waje kan taimakawa tsageru
- Gwamnatin ta ce, ya kamata mazauna kasashen waje su taimakawa gwamnati don ci gaban kasa
- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da kungiyar NIDO
Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya gargadi kungiyar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDO) kan daukar nauyin kungiyoyin 'yan aware.
Lai Mohammed ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar NIDO, reshen Burtaniya ta kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata, 27 ga watan Yuli.
Ministan ya ce abin takaici ne yadda kungiyoyin 'yan aware da ke fafutuka a duniya kuma suke amfani da wasu mambobin NIDO wajen yada labaran karya game da kasa Najeriya.
Ya ce wani abin damuwa ma shi ne yadda kungiyoyin 'yan awaren ke dogaro da gudummawar kudade da wasu mambobin NIDO ke bayarwa don gudanar da ayyukansu na barna.
Ministan ya bukace su da su taimaka wa kokarin gwamnati maimakon yada labaran karya da kuma yada “karya" na zarge-zargen cin zarafin addini, wariyar siyasa, da cin zarafin bil adama.
Jaridar Cable ta yanko inda ministan ke cewa:
"Abin takaici ne da kunya yadda wasu 'yan Najeriya mazauna kasashen waje har yanzu suka dogara da dandalin da ke yada labaran bogi da labaran karya game da Najeriya.
“Don haka, ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga NIDO da ta kwace wannan shiri daga wadanda suka kudiri aniyar bakanta sunan Najeriya a cikin wasu kasashe.
“A matsayin ta na kungiya mai tsari da kuma kyakkyawar alaka, ina rokon NIDO da ta yi hada kai da kungiyoyin gwamnati, kungiyoyin majalisu da cibiyoyin tunani na duniya da ke manyan biranen duniya don taimakawa wajen sauya labarin.
“Ina kuma rokon su da su guji kungiyoyin 'yan aware, masu tayar da kayar baya da masu son tayar da zaune tsaye wadanda ke da niyyar tura labaran karya don su nuna Najeriya na cikin mummunan yanayi.
"Ba ni da wata shakka cewa za ku dauki wannan kiran da mahimmanci kuma ku yi duk abinda za ku iya don canza labarin zuwa mafi kyau."
Lai Mohammed ya amince da cewa Najeriya na fuskantar kalubale
Ministan ya ce gwamnati ta amince da kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman a bangaren rashin tsaro, kuma tana “kokari” wajen ganin ta magance su.
Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na sake yin wani aiki tare da kara yin kokarin diflomasiyya don dakilewa da kuma juya akalar labarun karya kan Najeriya, baya ga dakile yaduwar farfagandar kin jinin gwamnati.
Lai Mohammed, duk da haka, ya yaba wa mambobin kungiyar NIDO ta Burtaniya saboda kishin kasarsu da kuma “haskaka kasar da kyau”.
Jerin sabbin manyan laifuka 3 da jamhuriyar Benin ke tuhumar Sunday Igboho akai
Ibrahim Salami, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Igboho ya bayyana cewa an bijiro da sabbin tuhume-tuhume a kan Sunday Igboho a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, yayin zaman kotu, jaridar The Punch ta ruwaito.
Kanu da Igboho: Kungiyar arewa ta dau zafi, ta bayyana abun da ya kamata FG ta yi wa ‘yan bindiga da makiyaya
Wadannan su ne uku daga cikin manyan laifukan da gwamnatin jamhuriyar Benin ke tuhumar Igboho akai:
- Hijira ba bisa ka'ida ba
- Hadin baki da jami'an shige da fice
- Kokarin haifar da tarzoma
PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya
A wani labarin, Jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din, jaridar Punch ta ruwaito.
PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.
PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.
Asali: Legit.ng