Cikakken jerin manyan jami'an 'yan sanda 24 da IGP ya tura wasu shiyyoyin Najeriya

Cikakken jerin manyan jami'an 'yan sanda 24 da IGP ya tura wasu shiyyoyin Najeriya

 • Sufeto-janar na 'yan sanda ya ba da umarnin aikawa mataimakan sufeto janar ga shiyyoyi a kasar
 • Rahoton Legit ya bayyana idan aka tura jami'an tare da bayyana wa dalla-dalla inda kowa zai kasance
 • A ranar Talata ne kakakin rundunar 'yan sanda ya fitar da sanarwar dake nuna wannan sabon umarni

Usman Alkali Baba, Sufeto-Janar na ’Yan sanda (IGP), ya ba da umarnin aikawa tare da sauyawa mataimakan Sufeto-Janar na 'Yan sanda 24 (AIGs) mukamai da kuma wuraren aiki na shiyyoyi.

A cewar wata sanarwa da Legit.ng ta samo a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda, CP Frank Mba, sauya wuraren aikin ya dace da sabuwar manufar ci gaban 'Yan Sandan Najeriya.

Sanarwar ta nuna cewa AIG Bala Ciroma zai koma shiyya ta 7 Abuja yayin da AIG Usman Belel, AIG John Amadi da AIG Adeleke Adeyinka aka tura su zuwa FCID Annex Lagos, Maritime da shiyya ta 9 da ke Umuahia bi da bi.

Jerin Jami'an 'Yan Sanda da IGP ya tura jihohin Najeriya baki daya
Yayin nadin wani jami'i | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Ga jerin sunayensu:

 1. AIG SPU FHQ Abuja - AI Zaki M. Ahmed
 2. AIG Shiyya ta 4 Makurdi - AIG Mustapha Dandaura
 3. AIG CTU FHQ Abuja - AIG Dansuki D. Galadanchi, mni
 4. AIG Shiyya ta 17 Akure - AIG Okon Etim Ene, mni
 5. AIG 'Yan Sintiri FHQ Abuja - AIG Usman D. Nagogo
 6. AIG Shiyya ta 7 Abuja - AIG Bala Ciroma
 7. AIG Shiyya ta 9 Umuahia - AIG Adeleke Adeyinka Bode
 8. AIG Shiyya ta 13 Ukpo-Dunukofia Awka - AIG Muri Umar Musa
 9. Kwamanda Polac Wudil-Kano - AIG Lawal Jimeta Tanko
 10. AIG FCID Annex Lagos - AIG Usman AlHassan Belel
 11. AIG DOPS FHQ Abuja - AIG Adebola Emmanuel Longe
 12. AIG Sashen Zuba Jari FHQ Abuja - AIG Musa Adze, fdc
 13. AIG DICT FHQ Abuja - AIG Philip Sule Maku, fdc
 14. AIG Shiyya 6 Calabar - AIG Usman Sule Gomna
 15. AIG Hadin gwiwa - AIG Adamu Usman
 16. AIG Shiyya ta 3 Yola - AIG Daniel Sokari-Pedro, mni
 17. AIG DTD FHQ Abuja - AIG Ahmed Mohammed Azare
 18. AIG FCID Annex Kaduna - AIG Maigana Alhaji Sani
 19. AIG Shiyya ta 12 Bauchi - AIG Audu Adamu Madaki
 20. AIG Maritime Lagos - AIG John Ogbonnaya Amadi, mni
 21. AIG Shiyya ta 8 Lokoja - AIG Ede Ayuba Ekpeji
 22. AIG Armament FHQ Abuja - AIG Mohammed L. Bagega
 23. AIG Shiyya ta 15 Maiduguri - AIG Bello Makwashi
 24. AIG Bangaren ayyuka FHQ Abuja - AIG Balarabe Abubakar

Manufar sauye-sauye da sabbin aikewar

Legit.ng ta tattaro cewa IGP Alkali Baba ya tabbatarwa da kasa cewa aikawar da sauya manyan jami’an 'yan sanda zai kara taimakawa wajen jagorantar sabon hangen nesan 'yan sanda a kasar.

Ya bayyana cewa wannan sabon tsarin na 'yan sanda, a tsakanin sauran abubuwa, an shirya shi ne domin inganta ayyukan 'yan sanda a duk fadin kasar da kuma magance barazanar tsaro a kasar.

'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu

A wani labarin, ‘Yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.

Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.

‘Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.

Biyu daga cikinsu sun sanya tufafin yahudawa. Wani mutum sanye da bakaken kaya harma yayi wa wasu manema labarai jawabi amma yayi magana ne da yaren Igbo, inji Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel