Badakalar NPA: Jam’iyyar PDP ta na so a hukunta Hadiza Bala Usman, a kai ta gidan yari

Badakalar NPA: Jam’iyyar PDP ta na so a hukunta Hadiza Bala Usman, a kai ta gidan yari

• Peoples Democratic Party (PDP) ta na so a hukunta Hadiza Bala Usman

• Jam’iyyar adawar ta dawo da maganar ne bayan jin an tsige Bala Usman

• PDP ta yi kira ga jami’an EFCC su binciki Bala-Usman da Rotimi Amaechi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira da a hukunta tsohuwar shugabar hukumar NPA da aka dakatar, Hajiya Hadiza Bala-Usman.

PDP ta na bukatar a hukunta Hadiza Bala-Usman ne a kan zargin da ake yi mata na cewa NPA ta karkatar da wasu Naira biliyan 165 a lokacin ta.

Premium Times ta ce PDP ta bayyana haka ne a wani jawabi da Kola Ologbondiyan ya fitar a garin Abuja, a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, 2021.

Dakatarwa daga ofis bai isa ba

Jam’iyyar adawar ta ce dakatar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Bala-Usman daga NPA bai isa ba, ya kamata a zartar mata da hukunci.

“PDP ta na bukatar a gaggauta hukunta shugabar NPA da aka dakatar, wanda yanzu an tsige ta, Hadiza Bala-Usman, a kan zargin satar N165bn.”

Baya ga haka, PDP ta yi kira ga hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta gayyaci tsohuwar shugabar ta NPA.

Rahoton ya ce ana zargin Bala Usman da wawurar Naira biliyan 15.18 da sunan ayyukan CSR da NPA ta yi.

Ayi bincike da kyau, EFCC ta binciki Minista

Hadiza Bala Usman
Shugabar NPA a Majalisa Hoto: nigerianports.gov.ng
Asali: UGC

Har ila yau, jam’iyyar ya bukaci a kara wa’adin kwamitin binciken da Mai girma Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya kafa domin ya binciki hukumar.

“Jam’iyyar ta na rokon EFCC ta fadada binciken ta zuwa ofishin Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wanda a ma’aikatarsa ne ake zargin NPA ta yi sata.”

Ologbondiyan ya ce PDP na tare da sauran jama’a, za ta cigaba da sa ido kan yunkurin da gwamnatin APC ta ke yi, na yin rufa-rufa da wannan lamarin.

A baya kun ji cewa tulin dukiyar hadimin Diezani Alison-Madueke, Jide Omokore, ya tara su na neman zama mallakar Najeriya yayin da ya koma kotu da EFCC.

Omokore zai iya rasa wasu daga cikin dukiyoyi, gidaje da kudin da ya tara a banki. Alkali ya ba hukumar EFCC dama ta rike dukiyoyin na-kusa da tsohuwar Ministar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel