Eid-el-Kabir: Bidiyo ya nuna Buhari yana tafiya zuwa filin Idi a Daura yayin daama'a ke taya shi murna
- Musulmai a Najeriya sun bi sahun takwarorinsu a duk fadin duniya domin yin bikin Eid-El Kabir na wannan shekarar
- Ba wanda za a bari, Shugaba Buhari ya yi tafiya zuwa mahaifarsa ta Katsina inda ya yi Sallar Eid-el-Kabir
- An gano Shugaban Najeriyan wanda ya sanya babbar riga launin shudi yana tattaki zuwa filin Idi a Daura
Shugaban kasa Muhammadu, a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, ya bi sahun ’yan uwansa a garin Daura, Jihar Katsina don yin Sallar Idi yayin da Musulmi ke bikin babbar Sallah.
Sallar wacce aka gudanar a filin Idi na Kofar Arewa ya samu jagorancin babban limamin garin, Alhaji Safiyanu Yusuf, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah
Shugaba Buhari wanda ya sha ado cikin Babanriga mai launin shudi ya isa filin Idi da misalin karfe 10:00 na safe. Da isarsa wajen aka tayar da sallar.
An yi wa Najeriya da Shugaban kasa addua
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, wanda tun farko ya iso filin Idin, ya gabatar da addu’o’i ga shugaban kasar da kuma Najeriya.
Ya kuma yi kira ga mazauna garin Daura da su rika tunawa da shugaban kasar a cikin addu'o'in su.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi
Daga baya Shugaban kasar da Sarkin Daura sun yi musayar goro da raguna kamar yadda Sallar ta tanada
Wani bidiyo da Muda TV ya wallafa a Facebook ya nuno shugaba Buhari yana tattaki kimanin kilomita 1 zuwa filin Idi.
Kalli bidiyon a kasa:
Bikin babban Sallah: Masarautar Daura ta bayyana matsayarta a kan Hawan Sallah
A baya Legit.ng ta ruwaito cewa masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta bayyana cewa an dakatar da Hawan Sallah a bikin Babbar Sallah da za a yi saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.
A cikin wata sanarwa da Danejin Daura, Abdulmumini Salihu ya fitar ranar Talata, 13 ga watan Yuli, ya ce Mai martaba Sarki Umar Faruq Umar ya ɗauki matakin ne saboda matsalolin tsaro da suka addabi yankin masarautar, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.
Sanarwar ta ce:
"A maimakon haka, za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba, bayan an kammala za a gudanar da addu'o'i na musamman a fadar mai martaba sarki don neman dawwamammen zaman lafiya.”
Asali: Legit.ng