Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Rasu a Kaduna
- Mai martaba Sarkin Chikun, Dr Danjuma Barde, ya riga mu gidan gaskiya
- Danjuma Barde ya rasu e a safiyar ranar Talata a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna
- Kungiyar cigaban Gbagyi, GDA, ta tabbatar da rasuwar sarkin ta bakin Peter Aboki
Allah ya yi wa Dr Danjuma Barde, sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya a ƙaramar hukumar Chikun ya rasu.
Leadership ta ruwaito cewa basaraken ya rasu ne a safiyar ranar Laraba
Rahotanni sun ce ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna bayan jinya.
DUBA WANNAN: Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa
Kungiyar GDA ta tabbatar da rasuwar sarkin
Peter Aboki, shugaban kungiyar cigaban Gbagyi, GDA, ya tabbatar da rasuwar basaraken a ranar Laraba kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Aboki ya ce:
"Mun rasa basaraken mu, ya dade yana fama da rashin lafiya. Ya rasu a safiyar yau a asibitin sojoji na 44 na Kaduna."
KU KARANTA KUMA: Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah
Sauya wa masarautar Gbagyi suna
A shekarar 2018 ne aka yi wa sarkin karin girma zuwa sarki mai sanda mai daraja ta daya bayan gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya canja wa masarautar suna daga 'Gbagyi' zuwa 'Chikun'.
Gwamnan ya kuma sauya lakabin sarkin daga 'Sa Gbagyi' zuwa 'Etsu Chikun', yana mai cewa hakan ya yi dai-dai da tsarin gwamnatin jihar na alakanta ikon sarakuna da yankinsu a maimakon kabila.
Amma, wannan sauyin sunan bai yi wa wasu daga cikin yan kabilan Gbayi dadi ba inda suka yi zargin cewa hakan wani yunkuri ne birkita tarihinsu da al'adunsu.
Tsohon Gwamnan Mulkin Soja Na Jihar Jigawa, Ibrahim Aliyu, Ya Rasu
A wani labarin daban, tsohon gwamnan na mulkin soja na jihar Jigawa, Birgediya Janar Ibrahim Aliyu (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a a Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da Habibu Nuhu Kila, mashawarci na musamman ga gwamnan Jigawa a bagaren kafafen watsa labarai ya fitar.
Asali: Legit.ng