Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun zargi shugaban kasa Buhari da mayar da fadarsa sakateriyar jam'iyya mai mulki
  • Kamar yadda gwamnonin suka ce, fadar ta zama wurin karakainar gwamnonin PDP da aka tirsasa zuwa APC
  • Gwamnonin sun zargin jam'iyya mai mulki da lalata tattalin arzikin kasa, mulkin kama-karya da murkushe kasar baki daya

Gwamnonin PDP sun caccaki Buhari

Gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da mayar da fadar shugaban kasa zuwa sakateriyar APC, Daily Trust ta ruwaito

A wani taro da suka yi a jihar Bauchi, gwamnonin PDP sun ce fadar shugaban kasa ta kowanne dan Najeriya ce amma an mayar da ita hedkwatar PDP inda ake ganin 'yan PDP da aka tirsasa zuwa APC akai-akai.

KU KARANTA: Ba harar tawagar Sarkin Kano aka yi ba, hatsari ne ya ritsa da su, Rundunar 'yan sanda

Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC
Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ina bukatar miji, Budurwa mai son daidaituwar 'yancin mata da maza ta koka

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: A karshe gwamnonin PDP sun yi martani, sun bayyana matsayinsu kan tura sakamakon zabe ta na’ura

Ana dabaru wurin janye gwamnoni zuwa jam'iyya mai mulki

Gwamnonin sun kara da kushe yadda ake amfani da wasu irin dabaru domin janye wasu daga cikin gwamnonin PDP inda ake tirsasa su zuwa jam'iyyar APC.

Sun zargi jam'iyyar mai mulki da lalata tattalin arzikin kasar Najeriya, mayar da Najeriya wurin kashe-kashe kuma tare da saka kasar cikin mugun hali da shugabanci mara kyau.

A fallasa ni idan na taba satar kudin jama'a, Uzodinma

Idan zamu tuna Legit.ng ta ruwaito yadda Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce bai taba satar kudin al'umma ba tun lokacin da ya kama aiki a matsayin gwamna a jiharsa.

The Nation ta ruwaito cewa a ranar Asabar 24 ga watan Yuli, gwamnan ya kallubalanci mutanen jihar su fallasa shi idan ya taba karkatar da kudaden al'umma.

An ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne a yayin taron masu ruwa da tsaki a Owerri.

Kara karanta wannan

Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP

Uzodinma ya ce a shirye ya ke ya amince a bincike shi domin ya nuna cewa bai yi almubazaranci da kudin al'umma ba.

A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane dake barna a babban birnin tarayya (FCT) suna cigaba da habaka saboda sun fara karbar kudin fansa ta hanyar amfani da asusun bankunansu, Daily Trust ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da mutane har kashi biyu a yankin Tungan Maje dake wajen garin. Miyagun sun koma yankin a ranar Laraba bayan sun sace mutum 6 daga yankin.

Sauran yankunan babban birnin tarayya da suka hada da Kuje, Bwari da Abaji suna fuskantar hauhawar lamarin garkuwa da mutane a watanni kadan da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel