Indimi ya zama sabon babban darektan kamfanin Oriental Energy Resources a Najeriya

Indimi ya zama sabon babban darektan kamfanin Oriental Energy Resources a Najeriya

  • Kamfanin Oriental Energy Resources Limited ta nada sabon babban darekta
  • Injiniya Mustafa Indimi ya zai jagoranci aikin Oriental Energy Resources Ltd
  • Ignatius Ifelayo da aka nada a shekarar 2013, yayi sallama da kamfanin yanzu

Babban kamfanin nan mai hako mai a Najeriya, Oriental Energy Resources Limited, ya nada Mustafa Indimi a matsayin sabon babban darekta.

Wannan sanarwa da kamfanin na Oriental Energy Resources Limited ya yi, ya fito ne daga bakin babban jami’in sadarwan kamfanin, Sam Umukoro.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN, ta ce Mista Sam Umukoro ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a garin Legas ranar Lahadi.

A cewar Umukoro, Mustafa Indimi ya karbi wannan aiki ne daga hannun Ignatius Ifelayo, wanda ya yi shekara bakwai ya na aiki da wannan kamfani.

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa Ifelayo ya yi digiri a kan ilmin man fetur a jami’ar Ibadan, ya yi aiki kasashen waje irinsu Amurka da Switzerland.

Kara karanta wannan

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

Shi kuma Mustafa Indimi ya kasance darekta a kamfanin kafin ya dare kujerar babban darekta.

Haka zalika sanarwar ta bayyana mana cewa Indimi ya na cikin majalisar manyan darektoci da ke sa ido a kan aikin Oriental Energy Resources Limited.

Mustafa Indimi
Shugaban Oriental Energy Resources, Mustafa Indimi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Sauran manyan darektocin sun hada da Ahmad Indimi, Ibrahim Indimi, Amina Indimi-Fodio, Goni Sheikh da shi karon kansa, Muhammad Indimi OFR.

Umukoro ya ce Indimi ya san kan aiki, kuma ana sa ran zai yi amfani da kwarewarsa wajen kasuwanci, wajen kai kamfanin man ga samun nasara.

Leadership ta ce sabon shugaban kamfanin ya yi digirinsa na biyu a harkar fasahar tace danyen mai a jami’ar Robert Gordon ta Aberdeen, kasar Scotland.

Oriental Energy Resources Limited

Ga wadanda ba su sani ba, fitaccen attajirin nan, Alhaji Muhammadu Indimi ya kafa kamfanin Oriental Energy Resources Limited a shekarar 1990.

A wannan shekarar ne gwamnatin sojin Janar Ibrahim Babangida ta ba kamfanin rijiyar man OPL 224

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng