Hatta Musa Ya Yi Hijira Saboda Fir'auna, Babu Laifi Don Igboho Ya Tsere, Afenifere
- Kungiyar Afenifere ta Yarbawa ta ce tserewar da Sunday Igboho ya so yi daga Nigeria ba laifi bane
- Afenifere ta ce idan za a iya tunawa ko Annabi Musa sai da Allah ya kawar da shi daga Fir'auna a Misra don kada ya zalunce shi
- Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin tarayya da yin watsi da yan bindiga da masu garkuwa yayin da ta ke musgunawa masu neman ganin an samu mulki na gari
Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta ce ba bu laifi tattare da tserewar da Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho ya yi, a kokarinsa na tsira da ransa da lafiya, The Cable ta ruwaito.
Afenifere ta yi wannan martanin ne game da kama Igboho da aka yi a Jamhuriyar Benin yayin da ya ke kokarin tserewa zuwa kasar Jamus.
Igboho na fuskantar shari'a ne a kotun daukaka kara ta Kwatano bayan kama shi a filin tashin jiragen sama na Bernardin a Kwatano.
Hukumar yan sandan farin kaya na DSS ta ayyana nemansa ruwa a jallo bayan kai samame gidansa da ke Ibadan a farkon watan Yuli.
A sanarwar da ta fitar ta bakin sakatarenta na kasa Jare Ajayi, Afenifere ta ce ba laifi bane Igboho ya tafi wata kasa domin tsira da ransa.
A cewar rahoton na The Cable, Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya na 'farautar masu neman sauki daga rayuwar matsi da ake a kasar' amma ta ki kula masu garkuwa da yan bindiga.
Gujewa zalunci sunna ce ta annabawan Allah, Afenifere
Kungiyar ta ce:
"Idan za mu iya tunawa an kawar da Musa daga idon Firauna da mukarrabansa a Misra. Annabi Muhammad (SAW) shima ya bar garinsa na Makka ya koma Madina don gujewa zalunci".
"Don haka, ba mu ga laifi ba idan Igboho ya nemi tserewa domin ya tsira da ransa ya sake damara da shiri.
"Duk hakan ma da bata faru ba da Sunday Igboho idan akwai gwamnati na gari sannan ba a tsangwamar mutane ba tare da wani dalili ba."
Malamin Sunday Igboho Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi ‘Layar Zana’ Ba, Ya Bari Aka Kama Shi
A wani labarin daban, Idris Oladejo, malamin Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana dalilin da yasa mai rajin kafa Kasar Yarbawan bai yi layan zana ya bace daga hannun jami'an tsaro ba.
Da ya ke magana da The Cable a kotun daukaka kara a Jamhuriyar Benin a Kwatano, malamin da aka fi sani da Imam Oladejo, ya ce Igboho bai bace daga hannun jami'an tsaro bane saboda matarsa da Kasar Yarbawa.
A lokacin da jami'an tsaro suka kai samame gidan Igboho a farkon watan Yuli, an ce dan gwagwarmayar ya ce amfani da asiri ne ya bace ba su kama shi ba.
Asali: Legit.ng